Batar Buhunan Garin kwaki: \’Yan Sandan Bayelsa Da Riba Suna Zargin Juna

0
705
MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba
RUNDUNAR \’yan sandan jihar Bayelsa da takwararta ta jihar Ribas sun
sanya kafar wando daya da juna sakamakon ce-ce-ku-cen da ya barke
tsakanin su saboda zargin da suke yi wa juna na batan wasu buhunan
garin kwaki guda hudu  da \’yan sandan FSARS suka  kama a kasuwar
Mbiama, karamar hukumar Ahoada ta yamma.
\’Yan sandan sun kama buhunan kwakin hannun wasu \’yan kasuwa
biyu  a kasuwar ta Mbiama,suka sanya a motar su kirar Hilux suka tafi
da su.
Wani wanda ya shaida lamarin mai suna Mashak Uyi ya shaida wa manema
labarai cewa shi ya ga lokacin da abin ya faru buhunna garin na wata
mace ce da kuma wasu mutane biyu kuma ya ga ma lokacin da masu kayan
suka rika bin motar \’yan sandan a guje.
Ya ce “na yi matukar  mamakin ganin wannan al\’amari na ga lokacin da wasu daga cikin \’yan sandan suka
tsilgo kasa daga motar su suka fara korar ,yan kasuwar da suka kasa
kayan su bakin hanya daga nan ne fa sai na ga sun fara dibar buhunan
garin kwakin suna sanyawa a mota”inji shi.
Uyi,ganau yaci gaba da cewa “ganin haka nefa ,yan kasuwar  da aka
debar wa kwakin suka bisu daga gudu suga manufar su ta saye ne ko kuma
yaya sais u ,yan sandan suka bude musu ido su koma ko su ba su jin
tsoro ne da haka \’yan sandan FSAR, suka tafi da buhunan kwaki hudu”.
An dai ta samun zargin juna tsakanin run dunonin biyu kuma ko wace
rundunar da wakilinmu na kudanci ya  tuntuba  jami,in hulda da jama,a
na rundunar jihar Bayelsa Butswart Asinim ya ce “ai Mbiama ba jihar
Bayelsa ba ne jihar Ribas ne don haka shi ba \’yan sandan rundunar su
ba ne don haka ba su da masaniyar har hakan ma ya faru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here