Jami\’an Kwastan Sun Kama Motocin Biliyan 1.76 A Ikoyi

0
673

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

A kokarin dakile ayyukan masu fasa kwaurin kayayyaki domin shigowa da su cikin Nijeriya ba bisa ka\’ida ba shiyyar kudu maso Yamma ta kame motocin alfarma da ake kira Jif guda 51 da kudin su ya kama Biliyan daya da Miliyan dari bakwai da daya.

Su dai jami\’an hukumar ta kwastan shiyyar Legas sun bayyana cewa sun samu labarin cewa akwai wadannan motoci ne a cikin wani gida a unguwar masu kudi ta Ikoyi, kuma nan da nan suka himmatu da gudanar da aiki.

Kasancewar motocin na alfarma kirar wannan shekarar guda 51 an shigo da su ta barauniyar hanya ne ya sa dole su gudanar da aiki.

\”Da akwai wadansu motocin hudu masu sulke wadanda idan za a shigo da su sai an nemi izini daga mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro\”

Akwai kuma karin wadansu motocin da aka shigo da su ta barauniyar hanya guda hudu su ma duk an kame su.

Kudin da ya dace a biya na haraji a samu a wadannan kaya ya kai Miliyan 20 Kuma kowace daya kudinta na kamawa daga Miliyan 20 zuwa 40 don haka ba kananan motoci ba ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here