Malaman Firamare: Ba Gudu Ba Ja Da Baya Wajen Daukar Sababbin Malamai

0
653
 Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
GWAMNAN Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa\’i, ya bayyana cewa batun sake daukar Malaman makarantar da za su koyar a Firamare da ke fadin Jihar ba gudu ba ja da baya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da kafofin yada labarai na rediyon Nagarta da sauran kafafen FM masu yada shirye shirye a gajeren zango da ke cikin garin Kaduna.
Malam Nasiru ya ce duk wani ce-ce-ku-cen da za a yi shi ba zai dame shi ba domin ya san abin da yake yi yana kokarin kawo gyara ne kuma saboda Allah yake yi.
\”Kamar yadda kowa ya sani ne dole a kwai gyara mai yawa a cikin harkar koyarwa kuma sai an gyara sannan zai gyaru a samu nasara, ta yaya shugaban Malaman Firamare zai dauki dansa ya kai makarantar kudi bayan ga wurin da yake koyawa \’ya\’yan jama\’a?
Ya ci gaba da cewa bana son in fadi zabe amma duk da haka sai an tabbatar da gyara na san wani Gwamnan da ya yi kokarin kawo gyara aka hada kai da Malaman makaranta a Jihar sa aka kayar da shi zabe, wai don kawai ya ce a gyara.
\”Da akwai wata mata da ta zo da takardar shaidar kammala karatu ta karanta ilimin sanin yana yi da fasalin kasa da itatuwa da ake kira Geography amma a wajen tantancewa aka ce mata ta fadi yadda ake rubuta sunan darasin da ta karanta ta kasa kuma ga takardar kammala karatu a hannunta
Kuma da akwai wadansu yara da aka kai su karatun likita a wata kasa Jihar Kaduna ce ta dauki nauyinsu domin a samu ci gaba sai ga shi a yanzu sun ba Jihar Kaduna kunya domin sama da goma cikin Arba\’in sun kasa cin jarabawar wucewa aji na gaba wanda saboda haka dole za a dawo da su gida, Kuma hakan ya faru ne tun farkon karatun su domin aikin gurbatattun Malamai irin wadanda za mu gyara a yanzu, Kuma daliban nan duk suna da takardun sun ci jarabawar sakandare kafin mu tura su zuwa makarantar da suka kasa.
Ta yaya za a yi wa malamin makaranta jarabawar \’yan aji hudu ya kasa amsa tambayar?
Za kuma mu wallafa sunayen Malaman makarantar da suka ci jarabawar a jaridun Dailytrust da Leadership don haka duk wanda bai ga sunansa ba ya san shakka babu ya fadi jarabawa ne.
Don haka a matsayina na Gwamna Ina son yin kira ga daukacin Malaman da suka ci jarabawa da kada su amince a rude su har su shiga yajin aiki domain duk wanda ya shiga yajin aiki za a tabbatar an yi abin da Doka ta tanadar a kan lamarin.
Ba za mu dauki alkawari cewa za mu yi gyara ba sannan mu kasa bayan muna ganin ga gyaran da ya kamata a gyara domin ba zai yi kansa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here