Buhari Ya Gabatar Da Kasafin Kudin 2018 Na Naira Tiriliyan 8.6

0
622

Rabo Haladu Daga Kaduna

SHUGABA Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin kasa da ya kai Naira Tiriliyan 8.6 ga majalisar dokoki
A jawabinsa ga majalisar dokin kasar yayin gabatar da kasafin, Shugaba Buhari ya ce gwamantinsa tana tsammanin za ta samu kimanin Naira Tiriliyan 2.442 daga albarkatun mai.
Ya kara da cewa Najeriya tana hasashen cewa za ta sayar da gangar mai sama da miliyan biyu a kowacce rana.
Shugaba Buhari ya ce gwamnati za ta kashe Naira Biliyan 300 kan gyara hanyoyi a fadin Najeriya.
Muhammadu Buhari ya ce gwmnatinsa za ta ware Naira Biliyan 8.9 domin tashar samar da
wutar lantarki ta Mambila .
Yaya aka kashe kasafin 2017? Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta samu ta yi hanyoyin kwalta na sama da kilomita 766 a fadin kasar a kasafin kudin shekarar 2017.
Dan majalisa ya rasa mukami kan badakalar kasafin kudi
Shugaban ya ce baya ga inganta harkokin noma da samar da makamashi, gwamnatinsa ta mayar da hankali ne kan biyan basussukan ayyukan da gwamnatocin baya suka bari ga \’yan kwangila domin a kammala ayyukan samar da ababen more rayuwa .
Ya bukaci \’yan Najeriya da su kwana da tabbacin cewa gwamnatin kasar tana iya abin za ta iya yi domin ta samar da dauwamammiyar wutar lantarki ga \’yan kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here