HAJJIN BADI: AN NEMI MANIYATA SU FARA BADA KUDIN AJIYA A KUROS RIBA

0
772

MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba

JIHAR Kuros Riba ta yunkuro domin fara karbar kudin aikin hajjin shekara ta 2018. Ta hanyar asusun gata wanda ake sa rai duk wanda suke da niyyar zuwa tun daga yanzu zai fara bayar da kudinsa ta hannun hukuma kafin daga bisani kuma ita hukumar alhazai ta kasa ta sanar da yadda kudin kujera zai kama na hajjin mai zuwa, haka abun zai kasance
kowace jiha duk fadin kasar nan.
Alhaji Tanimu Hassan shugaban hukumar alhazai jihar Kuros Riba ne ya sanar da haka ga wakilinmu na kudanci.
Ya ce bana “hukumar alhazai ta kasa wato NAHCO ta bullo da hanyar samar wa kanta sauki wajen rajistar mahajjata wanda a shekara mai zuwa hukumar a duk fadin kasar maniyyaci zai yi rajista ta intanit wanda hakan zai magance matsalar  rikici da ake samu tsakanin hukumomin jihohi da mahajjata wajen biyan kudi da kuma tashin alhazai wanda a wasu jihohin ake zargin wasu shugabannin hukumar da yin rub da ciki ko wala-wala da kudin mahajjata.  A badi za a yi rajistar mahajjata ne ta e-rajista ta yadda ba za a samu zargin bacewar kudin duk wani wanda ya biya kudi ba”.injishi
Alhaji Hassan yaci gaba da cewa “hukumar har wayau ta shawarci dukannin shugabannin hukumar alhazai ta jihohi su fara karbar kudi adashin gata ga maniyyaci da akalla Naira Dubu 300 ko fiye ma in ya so
idan lokaci ya yi hukuma ta kasa ta sanar da kudin kujera idan ma mutum ya biya kudin ajiya fiye da yadda hukuma ta kayyade za,a amayar masa da kudinsa da suka yi rara.Ya yaba wa shugaban hukumar na kasa bisa namijin kokari da ya yi wajen inganta aikin hajiin da ya  gabata aka yi aka gama lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here