Shugaba Buhari Yana Cika Alkawuransa.-Kungiyar MSDGG.

0
679
Daga Jabiru A Hassan, Kano.
KUNGIYAR tabbatar da dimokuradiyya da shugabanci nagari wato MSDGG ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari yana cika alkawuran da ya yi wa al\’ummar Nijeriya a lokutan yakin neman zaben shekara ta 2015, idan aka dubi irin nasarorin da gwamnatinsa ke samu a fannoni daban-daban.
Shugaban kungiyar na kasa Alhaji Muhammad Ahmed Dan Garba shi ne ya sanar da hakan a zantawarsa da wakilin mu a Kano, inda ya nunar da cewa kasar nan ta gamu da shugabanci iri-iri sai dai shugabannin ba su yi abin da ya kamata su yi ba domin ciyar da kasa gaba illa wawure dukiyar kasa da kuma yin son zuciya lokacin mulki.
Ya ce idan har za a yi alkalanci, ko shakka babu shugaba Buhari zai samu cikakken yabo idan aka dubi abubuwan da ya yi cikin shekaru biyu da rabi da ya yi yana jagorancin kasar nan duk da cewa ya rika samun matsaloli na rashin lafiya a lokuta daban-daban, wanda hakan abin dubawa ne.
Alhaji Muhammad Dan Garba ya ba da misalai masu tarin yawa na irin nasarorin da shugaba Muhammadu Buhari ya samu wadanda suka hada da inganta yanayin tsaro a fadin kasa da saita tsarin tafiyar da aikin gwamnati da yaki da cin hanci da kuma bunkasa noma da kiwo domin wadata kasa da abinci.
Sannan ya bayyana cewa yana da kyau \’yan Nijeriya su rika yi wa shugaban kasa uzuri domin kuwa yana tufka ne wasu kuma suna warwarewa amma Alhamdulillahi har yanzu mafiya yawan al\’ummar wannan kasa na kowane bangare suna fahimtar haka, kuma suna sane da ire-iren mutanen da ke yi wa wannan gwamnatin zagon kasa domin a ce ta gaza.
Shugaban kungiyar ta MSDGG ya ce kungiyar tasu ta kammala wasu shirye-shirye domin fara gangamin wayar da kan al\’ummar kasar nan dangane da irin kyawawan manufofin gwamnatin ta Buhari ta yadda kowa zai fahimci inda ta dosa da alherin da ke cikin ta kafin gabatowar zabukan shekara ta 2019 idan Allah ya kai mu,tare da yin kira ga daukacin \’yan Nijeriya da su kara nuna goyon bayan su ga wannan gwamnati saboda kyawawan manufofin ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here