NOMAN DANKALI ZAI BUNKASA SAMAR DA ABINCI-USMAN DAN-GWARI

0
907
Jabiru A Hassan, Daga Kano.
WANI fitaccen manomi daga Jihar Kano Alhaji Usman B. Dangwari ya ce noman dankali zai taimaka wajen samar da abinci musamman a wannan lokaci da ake ciki na shirin bunkasa noma a wannan kasa tamu.
Ya yi wannan bayani ne a wata tattaunawa da suka yi da wakilinmu a gonarsa ta Kwanar Dangora, inda kuma ya sanar da cewa kafin ya fara jarraba noman dankali a wannan guri sai da ya duba yanayin gurin da yadda zai tunkari noman dankalin domin tabbatar da ganin za a iya noman dankali a wannan sashe.
Sannan ya nunar da cewa noma sana\’a ce wadda take da riba kuma yana da kyau al\’ummar Nijeriya su rungume ta sosai ta yadda kowa zai kasa kiran gwamnatin tarayya na shirin wadata kasa da abinci, tare da samun hanyoyi na dogaro da kai cikin nasara.
Alhaji Usman Dangwari ya kuma bayyana cewa a yankin Kwanar Dangora za a iya noma dankali mai tarin yawa idan aka dubi yadda yanayin kasar gurin take , kaa ya yi fatar cewa manoman wannan kasa za su ci gaba da jajircewa wajen bunkasa ayyukansu na noma da kiwo rani da damina, tare da fatar alheri ga daukacin manoman kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here