0
  858

  Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

  GWAMNAN Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana cewa babu wani muhimmin mutum da yake cikin APC da ya fice daga cikinta a halin yanzu.

  Gwamna Masari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da kafar yada labarai ta BBC mai yada shirye-shiryen ta da harshen Hausa.

  Masari ya ce hakika siyasa kamar shiga mota ce wancan zai iya shiga ya kuma sauka a wannan tashar sannan kuma daga nan wani ne zai hau shi ma ya sauka a wata tashar.

  \”Ka duba ka gani dukkan tsofaffin Gwamnonin yankin kudu maso gabas sun dawo cikin jam\’iyyar APC sannan tsohon shugaban majalisar dattawa daga wannan yankin ya dawo APC, kun ga akwai nasara kenan\”.

  Don haka ya ci gaba da bayanin cewa suna goyon bayan Buhari ya sake tsayawa takara, amma da akwai lokacin fara siyasa domin akwai sauran shekara daya da kusan rabi, don haka a yanzu ana ta gudanar da ayyukan ciyar da kasa gaba ne kurum. Kuma duk masu bayanan sake tsayawa takara idan lokacin ya yi kowa zai ji domin abu ne a fili za a yi ba a boye ba.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here