AKALLA MUTANE 8 NE SUKA RAUNANA A WANI HATSARIN MOTA A KAUYEN CHIKARA

0
727
Daga Usman Nasidi
KIMANIN mutane 8 ne suka samu raunuka daban-daban a wani hatsari da ya afku da tsakar ranar Jumma\’ar da ta gabata a wani kauyen Chikara da ke daura da babbar hanyar Abuja zuwa Lakwaja.
Wani makusanci da inda hatsarin ya faru ya bayyana cewa, da misalin karfe 3:12 ne kan wata karamar mota kirar Volkswagen mai dauke da lambar KJA 49 XU ya kwace, inda ta yi allon kafura bayan tayoyin ta sun fashe kuma ta fada cikin wani rami.
Ya ce \”yayin da tayoyin motar suka fashe wadda ke kan hanyar ta ta zuwa birnin Abuja daga Lakwaja, sai aka yi rashin sa\’a direban motar ya yi kuskuren taka birki, wanda hakan ya yi sanadiyyar motar ta yi allon kafura ta fada wani rami da ke gefen hanya.\”
Nan da nan jami\’an hukumar kula da lafiyar tituna ta kasa (FRSC), suka garzaya da wadanda suka raunata a wannan hatsari.
Bincike ya nuna cewa, akwai wani hatsarin da ya afku a ranar Lahadin da ta gabata daura da babbar hanyar Abaji zuwa Toto a kauyen Kekeshi, da misalin karfe 3:23 inda mutane suka samu manyan raunuka.
A yayin tuntubar shugaban jami\’an na FRSC reshen Abaji, ACC Olasupo Esuruoso ya bayar da tabbacin faruwar hadurran inda ya bayyana cewa, wannan hadurra sun afku samakon rashin bin ka\’idar tuki wadda dokar kasa ta tanadar, ya kuma ce an garzaya da wadanda suka raunata zuwa babban asibitin Abaji

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here