An Kashe Kimanin Mutane Hamsin a Wasu Kauyukan Jihar Zamfara

0
639

Rabo Haladu Daga Kaduna

MAZAUNA kauyukan Tungar Kafau, da Mallamawa, da Shinkafi da wasu kauyuka a jihar Zamfarar  suna cikin
zaman fargaba sakamakon wasu hare haren da wasu yan ta’adda suka kai musu tsakanin kwanaki biyu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane kusan hamsin a wadannan kauyukan a Zamfara.
Rahotanni daga shedun gani da ido sun ce an kashe mata ashirin da shida a kauyen Tungar Kafau kana aka kashe maza goma sha tara a wani samame da wasu \’yan ta’adda da ake zaton barayin shanu ne da suka saba kai wa mutane yankin hare hare.
Dokta Suleiman Shuaibu na kungiyar Amnesty International dan asalin wannan yanki ne, ya ce ya zuwa yanzu babu wani jami’in tsaro da ya kawo dauki ga mutanen yankin. Ya kara da cewar mutane wannan yankin sun dade suna fama da hare haren barayin shanu kuma hukumomi sun nade hannu babu wani takamaiman mataki da suke dauka na ganin kawo karshen wannan lamari.
Mutanen yankin sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da su gaggauata daukar matakin kawo karshen abin da suka kira kisar kiyashi da barayin shanu ke musu. Sun ce rashin daukar matakin hukuma zai tilasta musu daukar matakan kare kansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here