Fatsar Kwastan Ta Yi Wawan Kamu A Kaduna

0
746

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

A kokarin da hukumar Kwastan karkashin jagorancin Kanar Hameed Ali mai rataya keyi a tarayyar Nijeriya na ganin ta tsarkake baki dayan kasar daga ayyukan bata-gari musamman wadanda ke taka dokar shigowa da abubuwan da aka hana a shigo da su. Hukumar shiyyar Kaduna bisa jagorancin Usman Dakingari, ta samu nasarar kame wata babbar motar Tirela makare da magungunan sa maye irin su Tiramol da buhunan shinkafa da aka yi masu badda- bami a cikin buhunan wake.

Hakazalika hukumar ta kuma kama wata mota kirar Jif mai sulke da aka shigo kasar da ita ba bisa ka\’ida ba.

Kamar yadda Usman Dakingari ya bayyana sun bukaci takardar izinin shigowa da irin wannan mota mai sulke kasancewar sai mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro ya bayar da takardar umarnin shigowa da motar amma babu wannan umarnin.

Sun kuma kama shinkafar kasashen waje da aka hana shigowa da ita Nijeriya, amma wadanda suka yi kunnen- kashi da hanin sun sako shinkafar ne a cikin buhunan wake da ke bayar da alamar kamar wake ne ga wanda bai sani ba.

Dakingari ya kuma bayar da tabbacin cewa za su gabatar da magungunan da suka kama ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa domin tantancewa kamar yadda doka ta tanadar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here