KUNGIYAR  MATASA  KURAME SUN YI KIRA GA GWAMNATIN JIHAR KANO

0
673
 Jabiru A Hassan, Daga Kano.
KUNGIYAR  neman ci gaban Kurame matasa ta Jihar Kano watau \” Kano State Deaf Youth Advocacy For Development\” (KADYAD)  tayi kira ga gwamnatin jihar kano da ta rika sanya su cikin shirye-shiryen ta domin suma su amfana da kyawawan tanade-tanaden da take da su na bunkasa rayuwar al\’umma.
Shugaban kungiyar Malam Rabi\’u Aliyu shine ya yi wannan rokon a wata ganawa da suka yi da wakilinmu, inda ya nunar da cewa matasa kurame suna bukatar kulawar gwamnati musamman a wannan lokaci da ake ciki tare da fatan cewa gwamnan Jihar ta Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje zai  fara sanya su cikin dukkan wani tallafi da gwamnatinsa ke yi ta yadda su ma za su ci ribar dimokuradiyya kamar sauran al\’umma.
Ya ce sun kafa wannan kungiya ne domin su hada kawunan kurame matasa da ke fadin Jhar Kano, kana su kasance masu gudanar da harkokin su na rayuwa bisa tsari da mutun ta juna domin ganin sun cimma manufar kafa ta.
Malam Rabi\’u Aliyu ya kuma sanar da cewa suna da mambobi a wannan kungiyar har fiye da dubu biyar,amma babu wani abu da ake yi da su walau a gwamnatance ko ta hannun wasu kungiyoyi har su sanya zuciyar  samun wani taimako a matsayin su na \’yan Adam kuma masu hakki a gwamnati.
Don haka kungiyar take yin roko ga gwamnatin  Dokta Ganduje da ta dubi halin da suke ciki domin ta bullo da wani tsari na taimaka masu wanda a cewar kungiyar akwai matasa masu digiri da sauran takardun shaidar kammala karatu a fannoni daban-daban, inda kuma kungiyar ta  KADYAD ta yi amfani da wannan dama wajen yaba wa kokarin gwamnatin Jihar Kano na kyautata rayuwar al\’ummar jihar ba tare da nuna bambancin siyasa ko na ra\’ayi ba.

 

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here