DUK WANDA AKA SAMU DA LAIFIN SATA A HARAMTA MASA  SHIGA ZABE-KUNGIYAR MATASA.

0
625
Jabiru A Hassan, Daga  Kano.
KUNGIYAR matasa masu tace dimokuradiyya  reshen Jihar Kano ta bukaci hukumomin yaki da cin hanci na EFCC da ICPC da su gudanar da cikakken bincike kan duk wani dan takara da ke son shiga zabe a kowane mataki  domin tabbatar da ingancin sa.
Wannan kira ya fito ne daga shugaban kungiyar na jihar kano Malam Abdulkadir Dan Asabe a hirar su da Gaskiya Ta Fi Kwabo, inda kuma ya nunar da cewa yana dakyau dukkan \’yan takara su sami amincewa daga hukumomin guda biyu kafin ma jam\’iyyun nasu su ba su damar tsayawa kowace irin takara domin ganin an sami shugabanni na kwarai kuma masu amana.
Ya ce kasar nan tana cikin wani irin yanayi mai tayar da hankai inda ake barin mutanen da aka sani da cin amanar kasa kuma suna sake yunkurin neman shiga takara,wanda ko kadan haka ba zai taimaki kasar nan ba, sannan ya yi fatan cewa hukumar zabe ta kasa da ta jihohi su rika gabatar da \’yan takara da ake kai mata ga hukumomin yaki da cin hanci na EFCC da ICPC domin a tabbatar da nagartar su kafin gudanar da zabuka.
Daga karshe Malam Abdulkadir Dan Asabe ya yi amfani da wannan dama wajen yaba wa gwamnatin Jihar Kano saboda sanya ranar zaben kananan hukumomi da ta yi domin cika tsarin dimokuradiyya, tare da fatan cewa nan gaba kadan za a bai wa kananan hukumomin kasar nan cikakken \’yancin su kamar yadda abin yake a baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here