APC TA GUDANAR DA ZABEN ‘YAN TAKARAR SHUGABANNIN KANANAN HUKUMOMIN FILATO  

  0
  954

   Isah Ahmed, Jos 

  A shirye shiryen da ake yi, na gudanar da zaben shugabannin  kananan hukumomin jihar Filato 17. Wanda za ayi a ranar 17 ga watan 2 na sabuwar shekara mai zuwa. Jam’iyyar APC reshen jihar  ta gudanar da zaben wadanda za su tsaya mata a wannan zave, a ranar asabar din da ta gabata.

   

  Wakilinmu ya gane wa idonsa yadda wakilin jam’iyyar masu zabe suka jefa kuru’unsu a cikin tsari batare da samun wata damuwa ba, har aka kammala zaben, a wuraren da aka gudanar da zaben a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Bassa.

  To amma wakilin namu yaga yadda aka tsaurara makatan tsaro a wajen da aka gudanar da zaben a karamar hukumar Jos ta Arewa.

  Tuni aka sami sakamakon zaben a kananan hukumomi 15 da aka gudanar da zaben. A karanar hukumar Jos ta Arewa an zabi Alhaji Shehu Bala. A yayin da aka zabi Mista Chindo Gona a karamar hukumar Bassa.

  Sauran wadanda aka zaba din sun hada da Mista Choji Dachung a karamar hukumar Jos ta kudu, Miskoom Alex a karamar hukumar Shendam, Ado Abubakar a karamar hukumar Wase, Amos Kparmim a karamar hukuma Langtang ta Arewa, Ibrahim Agwom a karamar hukumar Jos ta gabas, Isaac Kwallu a karamar hukumar Quan Pan,Ezekiel Mandyau a karamar hukumar Barikin Ladi, Lawrence Danat a karamar hukumar Mangu.

  Har’ila yau an zabi John D. Damap a karamar hukumar Panshin, Emmanuel Wambutda a karamar hukumar Kanke, Yusuf Manchen a karamar hukumar Bokkos, Gwallson Mafeng a karamar hukumar Riyom da Ezekiel Vongap a karamar hukumar Mikang.

  Da yake zantawa da ‘yan jarida sakataren jam’iyyar ta APC a jihar Filato Alhaji Bashir  Musan Sati ya bayyana matukar farin cikinsa kan yadda aka gudanar da zaben lafiya.

  Ya ce a kananan hukumomin Kanam da Langtang ta kudu da ba a sami gudanar da zaben ba, nan gaba za a bayyana ranar da za gudanar da zaben.

   A zantawarsa da wakilinmu kan wannan zabe tsohon dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazavar Jos ta arewa da Bassa Honarabul Lumumbar Dah Adeh ya bayyana cewa tun da aka dawo  mulkin damakaradiya a jihar Filato, ba a taba zaben ‘yan takarar jam’iyya kamar irin wannan ba, wajen yin adalci.

  Ya ce an tsara wannan zabe yadda ya kamata, ta yadda ba za a sami wata matsala ba.

  ‘’Wannan zabe ya banbanta da sauran zabubbukan tsayar da ‘yan takarar da aka yi a baya. Babu shakka yadda aka gudanar da wannan zabe zai bai wa jam’iyyar APC damar lashe wannan zabe a dukkan kananan hukumomin jihar nan’’.

  Shi ma a zantawarsa da wakilinmu kan wannan zabe wani jigo ta jam’iyyar APC kuma Garkuwan al’ummar Hausa Fulani na yankin Pengana dake karamar hukumar Bassa Alhaji Ya’u Bala PJ Jingir ya bayyana cewa an yi zabe mai tsafta a wannan zabe da aka gudanar. Ya ce a wannan zabe an baiwa talakawa dama sun zabi ‘yan takarar da suke so, batare da tursasawa kowa ba. Ya ce dama gwamanan Filato Simon Lalong  yace kowa ya je ya nemi jama’a shi ba shi da wani dan takara.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here