HUKUMAR BUNKASA MASANA’ANTU TA NIJERIYA TA HORAR DA MANOMAN MASARA DABARUN HARKOKIN KASUWANCI

  0
  724

  Isah  Ahmed, Jos

  HUKUMAR bunkasa kananan masana’antu ta Nijeriya [SMEDAN] ta shirya taron horar da manoman masara dabarun harkokin kasuwanci a cikin amfanin gona na masara a garin Saminaka dake  karamar hukumar Lere  a Kaduna.

  Da yake jawabi a wajen bude taron horar da manoman manajan hukumar a ofishin hukumar dake Kaduna, Badamasi Ya’u Barau  ya bayyana cewa sun zabi karamar hukumar Lere ne wajen gudanar da wannan shiri, ganin cewa ita ce kan gaba a harkokin noman masara a kasar nan.

  Ya ce jihohi 14 ne hukumarsu ta dauka don koyawa manoma dabarun harkokin kasuwanci a cikin kayayyakin amfanin gonar da suke nomawa don su dogara da kansu. Ya ce gudanar da wannan shiri ba manoma kadai zai taimakawa ba, har ma’aikata  zasu iya rike wannan shiri a matsayin abin da zasu dogara da kansu.

  Ya ce a wannan shiri  an debi mutum 50 a kowace jiha kuma an zabi kayayyakin amfanin gona daban daban wajen gudanar da shirin.

  ‘’ A jihar Kaduna an dauki noman masara don haka muka  dauki qaramar hukumar Lere a matsayin inda zamu koyawa manoman masara yadda ake harkokin kasuwanci a amfanin gona na masara’’.

  Ya yi  kira ga wadanda suka shiga wannan shiri su mayar da hankali kan abubuwan da aka koya masu domin su cigajiyar shirin.

  A nasa jawabin jagoran wadanda suka amfana da wannan shirin a karamar hukumar Lere Malam Ya’u Aliyu Lere ya bayyana cewa  mu dai mutanen karamar hukumar Lere mun gaji sana’ar noma ne.

  Ya ce sanin kowa ne a Nijeriya gabaki daya babu wata karamar hukuma da ta kai karamar hukumar Lere noman masara.

  ‘’Muna matukar farin ciki kan kawo wannan shiri.Kuma  da yardar Allah zamu yi amfani da dukkan abubuwan da aka koya mana a wajen wannan taron bita’’.

  Shima a nasa jawabin wani shugaban manoma Alhaji Tasi’u Bako Na Bawa Saminaka ya bayyana cewa wannan  shiri  da gwamnatin tarayya ta kawo  zai taimaki manoma wajen sarrafa kayayyakin amfanin gonar da suke nomawa.

  Ya yi kira ga gwamnati ta cigaba da tallafawa manoman kasar nan ganin cewa yanzu hankulan al’ummar Nijeriya ya koma kan harkokin noma.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here