AN NEMI GWAMNA GANDUJE YA FARFADO DA AYYUKAN INUWAR JAMA\’AR KANO

0
761
Jabiru  A Hassan,Daga Kano.
AL\’UMMAR  jihar Kano sun roki gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje da ta sake farfado da ayyukan kungiyar inuwar jama\’ar Kano waffa aka fi sani da \” Kano Forum\” saboda muhimmancin da take da shi ga al\’umma ta kowane fanni.
Wannan roko ya fito ne daga wasu al\’uma da wakilin mu ya tattauna dasu kan kungiyar wadda ta jima tana yiwa al\’umar jihar kao hidima musamman kan sha\’ann ilimi da samar da kayayyakin aiki ga makarantun jihar Kano manya da kanana.
Malam Salihu Ahmed Dawaki ya ce ko shakka babu inuwar jama\’ar kano tayi aiki a fannin ilimi tare da gudanar da tsare-tsare na kyautata yanayin koyo da koyarwa a makarantkun firamare da na gaba da firamare amma yanzu shiru ake ji babu wani abu da ake gudanarwa kamar yadda aka saba a baya.
Sannan ya ce har yanzu akwai mutane amintattu dake ciki kungiyar kuma suke fatan ganin an sake farfado da ita da karfafa mata gwiwar yin abubuwa na taimakon al\’umma a fannoni daban-daban kamar kula da lafiya da koyar da sana\’o\’i  ga mata da matasa da kuma samar da yanayi mai kyau ga ci gaban ilimi da noma.
Shi ma wani dalibi wanda ya taba amfana da aiyukan kungiyar Abubakar Musa Ibrahim ya ce, gaskiya lokaci ya yi da gwamnatin Ganduje za ta farfado da wannan kungiya mai amfani ta yadda za ta ci gaba da ayyukanta fiye da abin da ta yi a baya, inda kuma ya yi kira da babbar murya ga al\’ummar jihar ta Kano musamman  masu iko da su taimaka wa inuwar jama\’ar Kano kamar yadda auka saba domin ta ci gaba da aikace-aikacen ta na taimaka wa fannoni daban-daban.
Bugu da kari,wata daliba mai suna A\’ishatu Ahmed ta bayyana cewa tana fata Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje zai farfado da inuwar jama\’ar Kano domin ta ci gaba da aikin ta kamar yadda ta saba, tare da samar mata da dukkanin abubuwan da ake bukata na tafiyar da ayyuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here