JARABAWAR MALAMAI: Babu Malamin Da Gwamnatin Katsina Za Ta Kora—Kwamared Siwidi

0
675

Rabo Haladu Daga Kaduna

BIYO bayan shirin da gwamnatin jihar Katsina take yi na gudanar da jarabawar kwarewa ga daukacin malaman makarantar firamare, lamarin da ake ganin tamkar shirin korar malaman makarantar firamare ne ake yi.
Shugaban kungiyar Malamai ta kasa NUT Reshen jihar Katsina Kwamared Suwidi Hassan Dayi. ya karyata jita-
jitar da ake yadawa ana cewa gwamnatin jihar Katsina za ta yi wa malaman makaranta jarabawa domin ta kori wasu.
Ya ce malaman jihar Katsina masu hazaka ne, suna aiki tukuru kuma Sun rike aikin su. Shugaban ya ce gwamnati shirye take ma wajen kara bullo da shirye -shirye domin inganta koyo da koyarwa a jihar Katsina baki daya.
Sannan ya jinjina wa Gwamna Aminu Bello Masari a kan yadda yake aiki tukuru don kawo ci igaban ilimi a
jihar Katsina.
Suwidi Hassan ya kara da cewa wannan gwamnatin ta ba fannin ilimi kaso mafi tsoka a cikin kasafin kudi na shekara ta 2018 wanda hakan ke nunawa babu abu mafi amfani a yau a idon gwamnati da ya wuce ilimi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here