HUKUMAR KIYAYE HADURRA (FRSC) A JIHAR YOBE NA DA RAHOTON FARUWAR HADURRA KIMANIN 149 CIKIN WATANNI 20

  0
  663
   Muhammjd Sani Chinade, DAGA DAMATURU
  KWAMANDAN Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen Jihar Yobe, Daniel D. Sayi ya bayyana cewar, hukumarsa ta samu rahoton hadurra kimanin 149 a cikin watanni 20  wato daga shekarar 2016 zuwa karshen
  wannan shekara ta 2017 a dukannin fadin Jihar.
  Kwamandan hukumar ta kiyaye hadurran za bayyana hakan ne a yayin gudanar da wata bita ta musamman ga jami\’an hukumar na musamman a wannan shekara ta 2017 da aka gudanar a garin Damaturu yadda ya kara da cewar daga watan Janairu zuwa watan Oktoba na shekarar da ta gabata ta 2016 hukumar na da rahoton afkuwar hadurra kimanin 83 yayin da a wannan shekara ta 2017 aka samu kasa da hakan wato kimanin hadurra 66 wato da kashi 20 cikin dari.
  Don kwamandan ya ce raguwar yawaitar raguwar hadurran da aka samu ne bisa ga kokarin da gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam ke yi na samar da hanyoyin mota na zamani da kuma kokarin hukumarsa na ilimintar da masu abubuwan hawa dangane da dokokin amfani da abubuwan akan manyan hanyoyin mota da makamantan haka.
  Don haka ya kirayi masu abubuwan hanya na kasuwanci da na daidaikun mutane da su ci gaba da kula da lafiyar abubuwan hawansu musamman ta wajen kokarin daura belt kafin fara tuki tare kuma da gujewa amfani da wayar tafi-da-gidanka yayin tuki da kuma gujewa shan kayan maye, haka nan ya kuma gargadi masu abubuwan hawan da su guji gudin wuce kima yayin da suke tuki akan hanya da kaucewa shiga obatekin musamman a yayin tukin dare kai har ma da lokacin da ido na ganin wato da rana don kaucewa afkuwar hadurran da akullum kan haifar da rasa rayuka da jin munanan raunuka da asarar dukiyoyi.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here