BABU WANDA YA KAMATA YA SHUGABANCI KASAR NIJERIYA KAMAR SULE LANIDO-NAFI’U JOS

0
682

 Isah Ahmed Jos

SHUGABAN kungiyar matasa magoya bayan tsohon Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya tsaya takarar shugabancin kasar nan, a shekara ta 2019  karkashin jam’iyyar PDP [NLYMGG] na shiyar jihohin arewa ta tsakiya  Nafi’u Ya’u Jos, ya bayyanacewa babu wanda ya cancanci ya zama shugaban Nijeriya kamar Alhaji Sule Lamido.

Nafi’u Ya’u Jos ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taro da wata kungiyar matasa masu fafutukar ganin Alhaji Sule Lamido ya tsaya takarar shugabancin kasar nan, a zaben shekara ta 2019 reshen jihar Filato ta shirya a garin Jos.

Ya ce a duk gwamnonin da suka yi mulki a Jihar Jigawa, babu wanda ya yi aiki kamar Sule Lamido. Ya ce Sule Lamido ya yi  ayyukan raya kasa da dama a jihar Jigawa da suka hada da hanyoyin mota da samar da wutar lantaki da asibitoci da makarantu da ruwan sha.

‘’Alhaji Sule Lamido mutum ne mai hangen nesa, wanda  babu ruwansa da maganar nuna banbancin addini ko kuma banbancin kabila. Don haka idan al’ummar Nijeriya suka zabe shi, za su ci gajiyar mulkin dimokuradiyya’’.

A nasa jawabin shugaban kungiyar matasan masu fafutukar tsayawar takarar shugabancin kasar na Sule Lamido [SLYMN]  reshen jihar Filato Abdulhadi Abdullahi Cokali ya bayyana cewa wannan kungiya ce mai zaman kanta, wadda aka kafa ta watanni 10 da suka gabata. Ya ce wannan kungiya, wadda ta kunshi dukkan kabilun jihar Filato tuni ta kafa rassanta a dukkan mazabun jihar.

 ‘’Babban dalilin da yasa muka zabi mu goyawa Sule Lamido baya wajen ganin ya tsaya takarar shugabancin kasar nan, shi ne mun gano cewa babu wanda zai tafi da matasa idan ya zama shugaban kasar nan, kamar Sule Lamido’’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here