Kwastan Sun Kama Motocin Biliyan 1.3 A Legas

1
828
 Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
RUNDUNAR hukumar kula da shiga da fitar kayayyaki ta kwastan shiyyar Legas sun samu nasarar kame wadansu motocin alfarma guda 64 a unguwar Ikeja.
Shiyyar kudu maso yamma ta kai samame a wani gida a cikin garin Legas inda aka yi gini sannan aka sa waya aka yi kamar wani kango aka zuba manyan motocin alfarma a ciki.
Rundunar ta bayyana cewa ta samu nasara ne sakamakon cikakkun bayanan sirrin da suka samu daga masu ba su bayanai suna biyansu.
An dai kiyasta kudin motocin da cewa za su kai Naira Biliyan daya da dubu dari uku da suka kai 64 wanda a ciki har da motoci masu silke guda hudu.
WANNAN LABARIN MAIMAI NE.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here