SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI YA YI GODIYA GA AL\’UMMAR JIHAR KANO

0
701
Jabiru A Hassan, Daga Kano.
SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya nuna matukar godiyarsa bisa yadda daukacin al\’ummar  jihar Kano suka tarbe shi tare da yi masa rakiya tun daga filin jirgin saman Malam Amiu Kano har karshen ziyarar aiki da ya kai jihar.
Shugaba Buhari ya ce jihar Kano tana da muhimmanci a gare shi idan aka dubi irin soyayyar da ke tsakanin sa da al\’umar jihar tun ma kafin ya shiga cikin harkokin  siyasa, sannan ya kara da cewa  abin da aka yi masa a jihar Kano ya nunar da cewa har yanzu Kano tasa ce kuma babu mai raba shi da Kanawa a tafiya irin ta kaunar juna.
Shugaban kasar dai ya kai ziyarar aiki jihar Kano ta kwanaki biyu a karon farko tun bayan hawansa bisa kujerar shugabancin kasarnan,  inda aka yi masa tarba irin ta karramawa a filin jirgin sama na Aminu Kano kuma ka tsaye aka wuce zuwa gidan Sarkin Kano kana aka zarce zuwa kurkukun Kurmawa inda shugaban ya yi wa fursunoni 500 afuwa tare da yi masu nasiha domin su zamo mutane nagari.
Haka kuma shugaba Muhammadu Buhari ya yi abubuwa masu yawa a wannan ziyara da yakai jihar Kano ciki har da bude manyan  asibitocin nan da gwamnatin Ganduje ta kammala watau aaibitin Giginyu wanda aka sanyawa sunan shugaban kasar da kuma asibitin musamman na titin gidan namun daji wato Zoo Road da kuma sauran manyan ayyuka kamar hanyar kasa ta kofar ruwa da ake yi da kuma ta hanyar Madobi da aka kammala.
Mafiya yawan mutane maza da mata sun nunar da cewa wannan ziyara da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai  jihar kano  ta kara nuna cewa jihar tan cikin zuciyar sa duk da irin cece-kucen da wasu ke yi cewa ya ki zuwa jihar da aka fi nuna goyon bayansa a fadin kasar nan, inda wasu suka bayyana cewa har yanzu gwamnatin tarayya bata yi wa jihar aikin komai ba duk da irin soyayyar da Kanawa ke yi masa.
Wakilinmu wanda ya zagaya guraren da shugaban kasar ya ziyarta ya ruwaito cewa an sami cikakken tsari wajen  gudanar da ziyarar da kuma tabbatar da tsaro da doka yayin wannan ziyarar aiki ta kwanaki biyu da shugaban ya yi a jihar Kano cikin nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here