Sarkin Katagum, Kabir Umar Ya Rasu

1
1251

Rabo Haladu Daga Kaduna

SARKIN Katagum Kabir Umar ya rasu bayan ya sha fama da jinya.
Ya rasu ne a garin Azare jihar Bauchi.  za a yi jana\’izarsa a garin Zaki cibiyar masarautar Katagum.
Daga cikin \’ya\’yan da ya bari akwai Baba Kabir Umar wanda ya taba rike babban sakatare a ma\’aikatun gwamnatin tarayya da dama , wanda kuma yanzu shi ne hakimin Shira da ke gundumar Katagum.
Shugaban Majalisar Wakilan Yakubu Dogara ya bayyana rasuwar sarkin da cewa babban rashin ne ba ga iyalansa kadai ba. Inda ya ce, \”yana mika ta\’aziyyarsa ga iyalansa, da masarautar Katagum da jihar Bauchi baki daya\”.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here