A  WANNAN MAKON ZA A KAWO KARSHEN MATSALAR KARANCIN MAN FETUR A NIJERIYA-DANLADI PASALI

0
775

 Isah Ahmed, Jos

A yayin da ake fama da dogayen layukan motoci a gidajen man kasar nan sakamakon matsalar karancin man fetur  da ake fama da shi, Sakataren kungiyar dillalan man fetur ta kasa, Alhaji Danladi Garba Pasali ya bayyana cewa nan da karshen wannan mako za a warware wannan matsala, ta karancin man fetur a Nijeriya. Alhaji Danladi Garba Pasali ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ce a taron da suka yi, an tabbatar masu  cewa akwai manya manyan jiragen ruwa guda 6 da suka iso Nijeriya, dauke da man fetur  suna nan suna sauke mai a Fatakwal da Legas da Warri.

 ‘’Ina tabbatar maka daga nan zuwa ranar Juma’a  nan, za a ga raguwar layin motoci a gidajen mai. Domin tuni mun tura motocinmu zuwa wadannan wurare, domin su dauko mai su kai ko’ina a kasar nan, musamman arewacin kasar nan’’.

Alhaji Danladi Pasali ya yi bayanin cewa  sun umarci ‘yan kungiyarsu wadanda suke da manya manyan kamfanoni, su rika sayar da mai dare da rana a gidajen mansu. Domin a kawo karshen wadannan dogwayen layuka da ake fama da shi a gidajen man kasar nan.

Ya gargadi ‘ya\’yan kungiyar su guji   amfani da wannan dama, wajen kautar da man da aka ba su domin  kuntata wa mutanen kasar nan. Ya ce duk wanda  ya dauko mai, ya kai gidan mansa kada ya kauce da shi, domin duk wanda ya karkatar da mai, idan aka kama shi babu ruwan kungiyar.

‘’Mu kan mu bama jin  dadin wannan  matsalar karancin mai  da ke faruwa a kasar nan.Don haka mun tsaya don taimakawa hukumar kamfanin mai ta kasa [ NNPC] da gwamnati don kawo karshen wannan matsala’’.

Ya yi kira ga jama’a su kwantar da hankalinsu kan wannan al’amari, domin a halin yanzu motocin daukar mai sun fito daga kudanci dauke da mai,   zuwa kowanne lungu na kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here