GOBARA TA HALLAKA MAGIDANCI DA MATARSA DA ‘YA\’YANSA  UKU

0
1298

Isah Ahmed, Jos

WANI magidanci mai suna Malam Adamu  Yusuf da matarsa  Maryam Abdu da  yaransu uku  Abdul Adam dan shekara hudu da Ibrahim Adamu dan shekaru uku da kuma kanwarsu ‘Yar wata shidda, sun rasa ransu sakamakon  gobarar da dakin da suke kwance a ciki ya yi. Shi dai wannan al’amari mai ban tausayi, ya faru ne a layin Madaki da ke garin garin Bukur a karamar hukumar Jos ta kudu, da ke  jihar Filato, a daren ranar asabar da ta gabata.

Makwaftan gidan da wannan al’amari ya faru, sun bayyana cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe uku da rabi na daren ranar ta Juma’a, bayan da aka dauke wutar lantarki. Ana tsammanin rawar da wutar lantarkin ta yi, kafin a dauke ne ya haifar da tartsatsi a tsakanin wayoyin wutar lantarkin da aka bar su a bude ne, daga nan wutar ta tashi.

Wata makwabciyar dakin da wutar ta tashi, mai suna Maryam Lawal da ta kubuta daga wannan gobara tare da ‘yayanta biyu, ta bayyana cewa tana kwance sai ta rika jin iska tana kada rufin dakin da take. Tagar dakinta tana kadawa, sannan kuma sai ta rika ganin hayaki na shiga dakin nata. Ta ce nan take ta yi waje don ta ga daga ina hayakin yake fitowa, tare da ihun ankarar da makwafta su fito, don ba da taimako.

Ta ce an yi duk kokarin da ya kamata don ganin an balle kofar shiga dakin, don a fito da Malam Adamu Yusuf da iyalansa amma abin ya gagara. Sai da aka fasa bayan dakin, amma kafin a kai gare su ta Allah ta kasance a kansu.

Da yake yi wa wakilinmu karin bayani kanin mahaifin marigayi  Malam Adamu Yusuf mai suna Malam  Ibrahim Adamu ya bayyana cewa suna kwance a  cikin gida,  sai suka ji yarinya ta taho da gudu tana sallama tana cewa su zo ga daki ya kama da wuta. Da suka zo sai suka tarar dakin ya kama da wuta kuma  yana kulle.  Da kyar suka samu suka fasa dakin.

‘’Bayan da muka balle dakin sai na shiga cikin dakin, ina shiga sai naga yaro guda daya ya riga kone. Da na sake dubawa sai na gano hanun yarinyar wato kanwar yaron, na dauko ta na fito da ita.  Da na sake komawa cikin dakin, sai ya gano mai gidan da uwar gidan a jikin bangon dakin duk sun rasu, da haka muka fito da gawarwakinsu su biyar daga cikin dakin’’.

Ibrahim Adamu ya yi bayanin cewa bayan da muka fito da gawarwakinsu aka kai su masallaci, da gari ya waye aka yi masu jana’iza.

‘’Mun  mika wannan al’amari ga ubangiji domin mun yi imanin cewa  shi ne ya kawo wannan al’amari. Don haka  muna yi masu addu’ar  Allah ya gafatar masu’’.

Shi ma da  yake zantawa da wakilinmu mahaifin marigayi Malam Adamu Yusuf, mai suna Malam Yusuf Lantarki ya bayyana matukar bakin cikinsa da faruwar wannan al’amari, musamman ganin yadda ya shaku da jikokinsa.

Ya ce yanzu ya rasa jikokinsa guda uku a wannan gobara sai babbarsu Amina ta rage, wadda  a wannan daren ta kwana a dakin kakarta ne.

Ya ce babu shakka ya shaku da  wadannan jikoki nasa, domin  ko a ranar da wannan al’amari ya faru a gidansa suka yini.

‘’Amma a matsayina na musulmi na barwa Allah komai  kan wannan al’amari da ya faru.  Wannan yaro nawa da matarsa da jikokina kwanansu ne ya kare, kuma nima na san ko baxe ko bajima, zan tafi wajen da suka tafi’’.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here