An Kama Wata Mata Da Laifin Sayar Da Tagwayenta A Katsina

0
1006

Rabo Haladu Daga Kaduna

AN kama wata mata  bisa zargin sayar da tagwayen jariranta \’yan wata guda. Lamarin ya faru ne a jihar Katsina
Ana tuhumarta ne da laifin safarar yara, amma \’yan sanda sun ce za a iya kara tuhumarta da wasu laifukan na daban.
Rahotanni sun ce matar ta yi yunkurin sayar da \’ya\’yan nata mata tagwaye a kan Naira 350,000 ga wani mutum, wanda shi ne ya gaya wa \’yan sanda.
Matsalolin sayar da jarirai da safarar yara sun jima a Najeriya. Matar, \’yar shekara 30, ba ta yi wani bayani ba da aka gurfanar da ita a gaban kotu. Hukumar hana safarar mutane a Najeriya (NAPTIP) ta bayyana cewa binciken da ta
gudanar a shekarar 2011 ya nuna cewa a kan sayar da jarirai a kan $6,400.
A shekarar 2013, \’yan mata 17 masu juna biyu da jarirai 11 aka kubuto daga wani gida da ake haifar jarirai domin a sayar da su a jihar Imo.
Duk da nuna tsananin rashin jin dadi da jama\’a suka yi da kuma alkawarin gwamnati na cewa za ta dauki manyan matakai domin magance matsalar, iyaye mata a Najeriya sun ci gaba da siyar da \’ya\’yansu.
Shekara biyu bayan an bankado gidan haihuwar jariran a Imo, an kama wata mata yayin da take kokarin siyar da jaririnta a kan Dala 90 ko kuma Fan 67 a Jihar Kuros Riba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here