MUN RASA WAKILCI A MAJALISAR DATTIJAI, DA TA WAKILAI A DANDI, AREWA,ARGUNGU

0
935

Assalamu alaikum

   Da fatar dukkanin ma\’aikatanku suna cikin koshin lafiya

 ZUWAGA EDITA

Kasancewar zaben tumun daren da muka yi ya sa na gane cewa “yan siyasa ba kowane ba ne yake cikin alkawari, ni a zatona ba mu da wakilci, a majalisar, wakillai da ta Dattijai, idan muka yi la’akari da yadda, wadannan mutane babu wani abin a-zo-a-gani, da suka yi muna a yankunanmu, sabanin yadda wasu wakillai suke Goma na arziki ga Jama’arsu, babu wani abin more rayuwa da suka yi, ko shirin yin haka nan gaba,ko wayar wadanda suke wakilta ba su dauka, ballantana su ji koken jama’ar yankunansu,  tun lokacin da aka kare zabe, babu wanda ya sake sa su ga idanunshi, ba su zuwa gaisuwar mutuwa, babu maganar jajantawa idan wata annoba ta faru. Zargin da muke yi shi ne Dan majalisar wakillai na tarayya wato Dokta Hussaini Suleiman Kangiwa yana fama da tabin hankali.

 Shawarata ga jama’ar Kananan Hukumomin Dandi, Arewa, Argungu, da mu yi karatun ta natsu, mu sake fito da sababbin jama’ar da muke ganin za su shugabance mu, shugabanci nagari,idan muka yi la’akari da yadda Karamar Hukumar mulkin Dandi ta samu,wanda yake debe wa jama’arshi haki a ido, wannan ba karamin abin alfahari ba ne, irin wannan ya kamata mu samu a majalisar tarayya, ko majalisar Dattijan kasar nan, Jama’ar Dandi shaidu ne, mun gani mun kuma shaida,

  Daga

Shu\’aibu Muhammed Rijiyar Maikabi

Karamar Hukumar Dandi

Jahar Kebbi

09065810020

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here