Juyin-Juya-Hali Gwamna Tambuwal Ya Yi Wa Sashen Ilmin Jihar Sakkwato

0
624
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal Na Jihar Sakkwato dan takarar shugaban kasa a jam\'iyyar PDP

Daga Zubair A. Sada

GWAMNA Aminu Waziri Tambuwal ya ceto rayuwar al\’ummomin Jihar Sakkwato musamman ma yara kanana a bangaren ilmi inda ya kuduri aniyar yi wa bangaren juyin-juya-hali, sannan ya kirkiro kudurin doka da ta bai wa yara \’yanci ga ilmi a shekara ta 2016.

Muhammadu Sada Jayawa, wani matashin direban mota ne ya fadi haka a lokacin da suke zantawa da wakilinmu.

Sada Jayawa ya ce, Gwamnan ya yi haka ne domin ya bai wa yara \’yancinsu a fagen ilmi tare da kariya gare su. Ya ce Gwamnan shi ne na farko da ya aiwatar da irin wannan dokar a fadin tarayyar Najeriya, wadda tuni \’yan majalisar dokokin jihar suka zartar da ita ta zama doka.

Ya ce, Rt. Honorabul Aminu Tambuwal mutum ne mai hangen nesa, wanda ya gano cewa ilmin nan ga yara yana da muhimmanci, kuma gishiri ne na rayuwarsu ta duniya da lahira.

Daga karshe Sada ya ce, ko shakka babu su al\’ummar Sakkwato kwatansu, za su ci gaba da mara wa Gwamnan baya har zuwa karshen mulkinsa a shekara ta 2023 in sha Allahu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here