AL\’ UMMAR DAN RIMI SUN GODE WA GWAMNA GANDUJE

0
751
JABIRU A HASSA, Daga Kano.
AL\’UMMAR  Unguwar Dan Rimi da ke  yankin karamar hukumar Fagge sun nuna godiyar su ga Gwamnan Jihar Kano  Dokta Abdullahi Umar Ganduje saboda aikin titin da ya tashi daga \’yan babura zuwa Rafin Malam bisa la\’akari da muhimmancin da yake dashi ga al\’umomin da ke wannan yanki.
A zantawar da suka yi da wakilin mu, al\’umar ta Dan rimi sun bayyana cewa gwamnatin Ganduje ta cancanci yabo da godiya ta musamman saboda fara sabunta wannan titi da tayi kuma aiki mai kyau da inganci, sannan a cewar su, aikin yana tafiya cikin sauri da kyau tun lokacin da aka fara aiwatar dashi.
Limamin masallacin Ikhwanil Mustapha, Sheikh Malam Habib Sa\’idu yace sun dade suna ta addu\’ar samun wannan hanya amma ba ta samu ba sai a wannan lokaci na gwamnatin Ganduje, inda  a cewarsa, da yardar Allah za su nuna godiyar su ga gwamnan idan zaben shekara ta 2019 yazo.
Shi ma a nasa tsokacin, shugaban masu haya da babura masu kafa uku Malam Lawan Umar ya bayyana cewa idan aka kammala wannan titi za a sami yanayi mai kyau na zirga-zirgar ababen hawa, sannan za su kara samun kwarin gwuiwar biyan harajin da suke baiwa gwamnati  batare da tsaiko ba, inda ya yi fatan alheri ga gwamnatin Ganduje bisa wannan babban aiki da take yi masu.
Da yake nasa sakon, mai unguwar Dan  Rimi Alhaji Musa Sani,  ya ce akwai al\’ummomi masu tarin yawa da ke amfani da wannan titi na Dan Rimi, don haka yana fata gwamnatin Jihar Kano za ta hada shi da garin Ungogo  domin  amfanin al\’umomin da ke fitowa daga wannan sashe, inda kuma ya yi fatan alheri ga dukkanin wadanda suke da hannu wajen ganin an fara aikin wannan titi na Dan Rimi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here