Bikin Ranar Mata Ta Duniya Ba Ta Yi Armashi Ba A Jihar Yobe  

0
535
Gwamna Gaidam: Sha yabo katafila sarkin aiki
Muhammad Sani Chinade, Daga Damaturu
A bikin ranar mata ta duniya da aka gudanar a jiya Alhamis a Jihar Yobe da ma dukannin Jihohin kasar nan da ma duniya baki daya an samu wasu daidaikun matan da suka nuna cewar, su a Jihar Yobe matan na fuskanta matsalolin rayuwa sakamakon yadda suka samu kansu ciki sanadiyyar rikicin Boko Haram da Jihar ta yi fama da shi na tsawon lokaci wadda kai tsaye su ne suka fi fuskanta matsalolin.
Kan hakan wakilinmu ya samu ganawa da wata mata wacce ta nemi a boye sunanta, inda ta bayyana cewar, ita g ganinta babu abin da wannan rana ta mata ke tuna mata fiye da yadda a halin yanzu mata a Jihar Yobe ke shan bakar  wahala musamman su da  suka rasa mazajensu sakamakon rikicin Boko Haram wadda hakan ya sa ala tilas a mafi yawa-yawan
lokaci sai sun yi bara ko maula ko kuma aikin kodago in ya samu don su ciyar da kansu da yaransu marayu duk da dan tallafin da bai taka kara ya karya ba da suka samu daga wasu kungiyoyin kasa da kasa.
Don haka ne wannan mata ta ce, lalle akwai bukatar gwamnatocin jihohi da na tarayya da su  ma su shiga a dama da su don fitar da su daga wannan hali da suka samu kansu ciki.
Ita kuwa Malama Falmata  Aji wacce ta ce ita wannan rana ta mata babu abin da za ta ce illa, gwamnatin tarayya da jami\’an tsaron kasar nan su taimaka don ceto \’ya\’yansu matan makarantar Dapchi da \’yan kungiyar Boko Haram suka kwashe a kwanakin baya don gudin ci gaba da tursasa musu.
A cewar Malama Falmata matukar ba haka aka yi ba to kuwa lamarin kan iya haddasa shiga halin hawula\’i musamman ga mu mata iyayensu.
Alal hakika wannan biki na ranar mata ta duniya bai yi armashi ba a Jihar ta Yobe wadda hakan ba zai rasa nasaba da sace \’yan matan makarantar sakandaren kimiyya da fasaha ta garin Dapchi da \’yan Boko Haram suka yi wadda hakan ya sa ala tilas wasu iyayen ke cire yaransu daga wasu makarantun kwana dake Jihar don gudin abin da ya faru a baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here