Gwamnatin Tarayya Ta Kori Tsohon Mukaddashin Shugaban Hukumar NIA Daga Aiki

1
609

Rabo Haladu Daga Kaduna
KAMA daga majalisar wakilan  da masu fafutikar kare hakkin dan Adam a Najeriya tamkar kowa na cikin rudani a kan badakalar dake faruwa a hukumar leken asirin kasashen waje, NIA inda yanzu gwamnatin Buhari ta sallami tsohon mukaddashin shugaban hukumar daga aiki
Bayanai daga hedkwatar hukumar leken asirin kasashen waje ta Najeriya, wato, NIA, na cewa gwamnatin shugaba Buhari ta kori Ambasada Muhammad Dauda, tsohon mukaddashin shugaban hukumar, daga aiki, wanda kwanaki biyu da suka gabata jami\’an DSS suka yi wa gidansa kawanya.
Korar na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar wakilai ke binciken wata badakalar zunzurutun kudi na dalar Amurka miliyan 289 da kuma cancanta ko rashin cancantar nadin Malam Ahmed Rufai a matsayin shugaban hukumar ta NIA.
Abubuwan da ke faruwa da Hajiya Naja\’atu Muhammad, jami\’ar daya daga cikin kungiyoyin da ke kare hakkin bil Adama a Najeriya, ta bayyana cewa abin da aka yi abin kunya ne kuma ya kada ta. Ta ce shi Ambasada Muhammad Dauda yana aikinsa aka nada wani dabam ba tare da samunsa da wani laifi ba. Amma sai ga shi gwamnatin Buhari ta kore shi
daga aiki ma gaba daya.
Hajiya Naja\’atu ta ce bugu da kari sai ga shi Shugaba Buhari ya nada wani kwamitin bincike a karkashin shugabanci Babagana Kingibe wanda ake zarginsa da yi da sama da fadi da
miliyoyin dala.
Yayin da Majalisar wakilai ta fara bincike shi Muhammad Dauda ya fada ya ba Babagana Kingibe wasu kudi kuma akwai sauran kudi fiye da dala miliyan arba\’in. Muhammad Dauda ya ce za a yi sama da fadi da kudin saboda haka sai ya kai kara. Bugu da kari sai gwamnati ta nada wanda majalisa ta ce kada a nada a matsayin shugaban hukumar.
Shi ko Aminu Sani Jaji, shugaban kwamitin tsaro na majalisar wakilan wanda kwamitinsa ke gudanar da bincike akan badakalar NIA din, ya ce yana bukatar lokaci domin ya gudanar da bincike kafin ya yi magana.

1 COMMENT

  1. Allah yakyauta allah kuma yakaraba jamian tsaronmu nasara akan masu laifi gaskiya tafi kwabo bakaryabane maaikatan gaskiya tafi kwabo allahyakaramaku basira.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here