Ba Abin Da Manoman Sakkwato Za Su Ce Wa Gwamnatin Tambuwal Sai Sam-barka -Malami

0
610
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal sha kwaranniya

Daga Zubair Abdullahi

GWAMNATIN Aminu Waziri Tambuwal na ta shan sanya albarka daga bakunan dubban manomanta bayan da gwamnatin ta sayo kimanin takin zamani Tan Dubu dari uku  (30,000.) kuma ta rarraba wa manomanta a kan ragowar farashi mai rahusa, inda kowane manomi ya sami ragowar Naira Dubu biyu da dari biyar a bisa kowane buhun taki daya.

Kwamared Abubakar S. Malami mai shugabantar hukumar Ci Gaba Da Ayyukan Noma ta Jihar Sakkwato ne ya fadi haka ga manema labarai.

Malami ya ce, Gwamna Tambuwal har ila yau ya kaddamar da batun hayar Mota Tarakata ta noma a jihar a farashi mai sauki ga manoman. Ya kuma ware kudi har kimanin Naira Biliyan 3 domin ganin an yaki al\’amarin nan na rikicin makiyaya da manoma.

Haka kuma domin tabbatar da samar da aikin yi da rage radadin talauci, gwamnati ta kafa tsangaya ko kamfanin Nama Da Nono wanda kusan shi ne irinsa na farko a nan bangaren kasashenmu na Hausa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here