A SAKE FASALIN SANATOCI DA ‘YAN MAJALISAR WAKILAI-FARFESA DADARI

  0
  943

  Isah  Ahmed, Jos 

  Farfesa Salihu Adamu Dadari malami  ne a sashin bincike da nazarin aikin gona na jami’ar Ahmadu Bello, da ke Zariya kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu ya yi kira kan a sake fasalin  Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai ta tarayya a Nijeriya. Musamman kan irin makudan kudaden da ake biyansu albashi.

  Ga yadda tattaunawar da kasance

  GTK; Ya ya kake ganin yanayin yadda harkokin siyasa yake tafiya a kasar nan a halin yanzu, musamman ganin yadda ake tunkarar zabubbuka na shekara ta 2019?

  Farfesa Dadari; Wato yanayin yadda harkokin  siyasa suke tafiya, musamman a wannan lokaci da zabubbuka na shekara ta 2019 suke kara gabatowa a Nijeriya, akwai damuwa. Domin masu tsara dokokin Nijeriya ‘yan majalisunmu. Kuma ‘Yan majalisun Nijeriya  su kansu suna da matsala.

  Ni a ra’ayina a sake yiwa ‘yan majalisun dokokin Nijeriya fasali. Domin tun da suka tafi majalisa bamu ga tsarin da suka yi da zai fitar da Nijeriya daga matsalolin  da take ciki ba. Suna ta fadace fadace ne kawai.

  Kuma tsarin yadda ake biyansu albashi bai kamata ba. Saboda tsarin mulkin da Nijeriya take aiki da shi, na shugaba mai cikakken iko ba dole ne mu bi yadda kasar Amerika take tafiyar da wannan tsari ba. Domin kasar Amerika tafi mu arziki da neman dukiya. Don haka wajen biyan albashin ‘yan majalisa a Nijeriya, sai mu kamanta. Mu yi aiki da tsarin shugaba mai cikakken iko, amma kada mu ce zamu yi aiki da dukkan abubuwan da suke cikin wannan tsari domin tattalin arzikinmu ba zai iya daukar nauyin bin wadannan tsare tsare ba.

  Ya kamata mu tsaya mu yi wa al’ummar Nijeriya aiki da kudaden kasar, maimakon biyan ‘yan majalisunmu miliyoyin kudade.Kudin albashin da ake biyan dan majalisa daya a Nijeriya, a wata ya isa a xauki ma’aikata 300 zuwa 500, wannan bai  da ce ba.

  A gyara kudin tsarin mulkin Nijeriya ta yadda za a soke ‘yan majalisar dattawa, a bar ‘yan majalisar wakilai ta tarayya kadai, kuma a rika biyansu  kudaden zama kawai. Idan suka je suka yi zama a kowanne watanni uku,  suyi mako biyu su tattauna abubuwan da suka dami Nijeriya. Idan sun gama zama a biyasu kudaden zama kawai.

  Wannan zai hana yawan fadace fadace kan yadda kowa yake cewa sai ya je majalisa. Saboda makudan kudaden da ake bayarwa. Saboda haka mu sake duba tsarin mulkin Nijeriya kan maganar albashin ‘yan majalisa a Nijeriya.

  Ka duba muna da mutane sama da mutum miliyan 180 a Nijeriya, amma wadannan sanatoci da ‘yan majalisar wakilai  basu kai mutum 500 ba, amma suna cinye kudaden da za a yiwa al’ummar Nijeriya sama da mutum miliyan 180 aiki, wannan bai dace ba.

  GTK; To, ya ya kake ganin ayyukan da wadannan ‘yan majalisa suke yi?

  Farfesa; Dadari; Yan majalisun nan har ya zuwa wannan lokaci, basu yi ayyukan da suka kamata ba. Yanzu idan kaje ka tambayi dan majalisarku maye ya yi a mazabarsa? Ba zai iya nuna maka komai ba. Wadansu ma tun da suka je majalisa basa iya magana. Wasu ma basa zuwa majalisar, idan kaji sun je sai sun ji labarin cewa za a biya albashi. Irin yadda wasu  ma’aikatan kananan hukumomin Nijeriya suke yi, basa zuwa aiki sai sun ji labarin cewa za a biya albashi.

  Yanzu kamar sanatocin jihar Kaduna guda biyu  suna fada da gwamna, yau she ne zasu iya zama su yiwa jihar Kaduna aiki. Haka sauran ‘yan majalisar suke dukkansu ‘yan dambe ne, wato suna fada ne kawai ba aikin majalisa ba.

  Saboda haka muna kira ga ‘yan Nijeriya duk mutanen da suka ga sanatansu ko dan majalisarsu baya yi masu aiki, kada su saurare shi a zabe mai zuwa.

  Kuma ya kamata ‘yan Nijeriya su lura  ‘yan majalisun nan, suna zuwa suna sayen ‘yan mashina da kekuna suna raba masu ba, ba abin da ya kamata su yi masu ba ke nan. Idan aka dubi irin makudan kudaden da ake basu, don su zo su yiwa al’ummomin mazabunsu ayyukan raya kasa. Amma sun qi yin haka sai su zo suna sayen Babura da kekuna suna rabawa mutane.

  Yanzu a Nijeriya sanatoci  da ‘yan majalisar wakilai  ne matsalarmu. Don haka ya kamata a sake lale. Idan ba a sake lale kan ‘yan majalisar dattawa da wakilai ba, Nijeriya ta shiga uku. Domin babu yadda za ayi a cigaba a Nijeriya a wannan tsari na ‘yan majalisar dattawa da ‘yan majalisar wakilai.

  GTK; Maye zaka ce kan  dambarwa da ke  faruwa  yanzu, tsakanin ‘yan majalisar tarayya da hukumar zabe ta kasa INEC, kan fara zaben shugaban kasa a zaben shekara ta 2019?

  Farfesa Dadari; Wannan dambarwa da ake yi tsakanin ‘yan majalisar tarayya da hukumar zabe ta kasa INEC zalunci ne, ‘yan majalisar tarayya suke son su yi. Saboda sun ga, ba zasu iya komawa ba, don haka suke son a fara da zabensu, maimakon a fara da zaben shugaban kasa. Wannan gyara da suke son su yi, ba zai yuwu ba sai  dai idan za a sake gyara kundin tsarin mulkin Nijeriya ne gabaki daya.

  Maye yasa tun da suka hau basu ce zasu yi wannan gyara ba, sai yanzu da suka ga zave ya gabato?. Saboda haka muna kira ga shugaban kasa kada ya yarda ya sanya hanu, a wannan gyara da ‘yan majalisa suke son su yi.

  Gari ya waye saboda haka ba zamu yarda ba. A tafi da yadda tsarin mulkin Nijeriya ya tsara, mai ci yaci wanda zai fadi, ya fadi. Domin mun lura cutarmu kawai ake son ayi, kamar yadda aka saba. Nijeriya kasa ce mai arziki da yalwa don haka ya kamata ace muna cigaba, kamar yadda sauran kasashe suke yi a duniya.

  GTK; Idan muka dawo ga gwamnoni da ‘yan majalisun jihohin Nijeriya, ya ya kake kallon tasu tafiyar?

  Farfesa Dadari; Kasan da yake an sami rauni wajen sayar da mai a Nijeriya. Domin tun daga lokacin da wannan gwamnati ta hau kan mulki, farashin mai ya fadi a kasuwar duniya. Don haka muka tsinci kanmu a Nijeriya, sai dai gwamnati ta biya albashi kawai.

  Abin da muke magana shi ne gwamnonin da suka iya yin wani abu a Nijeriya, a halin yanzu sune wadanda suka iya samo kudaden shiga a jihohinsu. Irin wadannan gwamnoni  sun dan yi abubuwan da suka kamata a jihohinsu. Misali kamar jihohin Legas da Kano da Adamawa da Kaduna. Saboda haka wasu gwamnonin Nijeriya sun yi aiki, wasu gwamnonin kuma ko albashi basa iya biya.

  To yanzu irin waxannan gwamnoni da basu yi komai ba, maye zasu zo su fadawa al’ummomin jihohinsu?.

  Su kuma ‘yan majalisu na jihohi ya kamata su hada kai da gwamnoninsu ne su yiwa jama’a aiki, amma basa iya yin haka. Suna kokari ne kawai kan abin da za a basu, su sanya a aljihu.

  Don haka har yanzu siyasar Nijeriya muna cikin matsala.

  GTK; Maye zaka ce kan rikice rikicen da ake fama da su a jam’iyyun Nijeriya, musamman  jam’iyyun   APC da  PDP?

  Farfesa; Dadari; Wato wadannan rikice rikice da suke faruwa a jam’iyyun Nijeriya, alhaki ne ya kama ‘yan siyasar Nijeriya, domin yawaicinsu basu da gaskiya. Dukkan wadannan rikice rikice da suke faruwa wadansu ne suke son ayi da su, ko a basu wasu abubuwa, don su sami kuxi. Don haka ake samu wadannan rikice rikice.

  Yanzu misali kamar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar maye yasa ya bar jam’iyyar APC?  Ai ya bar PDP ya dawo APC ne maye yasa ya sake komawa PDP?. Irin wadannan masu son su sami mulki ne kawai, ba maganar su yiwa talakawan Nijeriya aiki ba.

  Amma wannan rikici alheri ne ga ‘yan Nijeriya domin duk wanda ya yi nasara, zai tsaya ya yiwa kasar aiki.

  GTK; Wanne sako ko kira ne kake da shi zuwa ga al’ummar Nijeriya?

  Farfesa Dadari; Abin da nake kira ga ‘yan Nijeriya shi ne mu natsu mu zabi mutanen kwarai, waxanda zasu yi mana wakilci nagari a zabubbuka masu zuwa. Wadanda suka yi, mun ga rawarsu mu watsar da su, mu sami sababbin jini ko dattawa wadanda zasu yi mana wakilci nagari.

  • Farfesa Salihu Adamu Dadari,,.jpg
   186.9kB

   

   


   

  • ,
  • or

   

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here