ZIYARAR SHUGABA BUHARI A JIHAR FILATO

  0
  911
  Shugaba Muhammadu Buhari

  Isah  Ahmed, Jos

  Shugaban kasa Muhammad Buhari ya kai  ziyara jihar Filato ta kwana biyu, a ranakun alhamis da juma’ar da ta gabata, don Kaddamar da ayyukan da gwamnan jihar Simon Lalong ya yi, tare da ganawa da al’ummar jihar.

  Shugaba Buhari ya sauka a filin saukar jiragen sama na Jos ne, da misalin karfe 11;50 na ranar ta alhamis.

  Gwamnan jihar Simon Lalong da gwamnan jihar Nasarawa Tanko Almakura da ministan matasa da wasanni Solomon Dalung da Sanata Joshua Dariye  da shugaban majalisar dokokin jihar da ‘yan majalisar wakilai ta tarayya da tsofaffin gwamnonin jihar da manyan sarakunan jihar ne suka tarbe shi, a filin saukar jiragen saman na Jos.

   

  \"Add

  Daga nan shugaba Buhari ya shigo garin Jos tare da dubban mutanen da suka tarbo shi. A inda yazo ya fara kaddamar da babbar hanyar Marabar Jama’a zuwa cikin garin Jos da babbar gadar saman nan  da ke sakateriya Jounction da tsohuwar gwamnatin jihar da ta gabata ta fara, gwamnan Lalong ya zo ya kammala.

   Daga nan shugaba Buhari ya ziyarci fadar shugaban majalisar sarakuna ta jihar, kuma Gbong Gwom Jos Da Gyang Buba.

  Da yake jawabi a lokacin da ya yi taro da masu ruwa da tsaki na jihar, a gidan gwamnatin jihar, Shugaba Buhari ya yabawa gwamna Lalong kan kammala ayyukan raya kasa da gwamnatin da ta gabata a jihar ta faro.

  Har’ila yau ya yaba wa gwamnan kan kokarin da ya yi wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar. Ya ce babu shakka gwamna Lalong ya yi kokari wajen ganin doka da oda ya dawo a jihar Filato.

  Hakazalika ya yabawa gwamnan kan kokarin da ya yi wajen biyan ma’aikatan jihar kudaden albashin da suke bi bashi.

   A nasa jawabin gwamna Lalong ya yi bayanin cewa a wannan ziyara da shugaba Buhari ya kawo jihar, zai ganewa idonsa irin nasarorin da gwamnatin jihar ta samu, duk da matsalolin rashin kudade da ake fama da shi a kasar nan.

   Gwamna Lalong ya ce a lokacin da muka qarbi shugabancin jihar nan, mun zo mun sami jihar a cikin yanayi na rikice rikice da suka yi sanadin asarar rayukan al’umma tare dukiyoyi masu tarin yawa. Ya ce mutane daga ko’ina suna tsoran zuwa wannan jiha, sakamakon wannan hali da jihar  ta shiga. Amma cikin yardar Allah muka sami nasarar magance wadannan matsaloli.

  ‘’Har’ila yau mun sami nasarar biyan  albashin ma’aikatan jihar nan na watanni 8  da bashin albashin malaman makaranta na watanni 7 da kuma bashin kudaden ‘yan fansho na watanni 12.

   

   

   

   

   

   

   Gwamna Lalong ya yabawa shugaba Buhari kan tallafawa jihohi da kudade don ceto su daga cikin mawuyacin halin da suka shiga, na rashin kudade.

   

  Ya ce babu shakka wannan tallafi ya taimakawa gwamnatin jihar Filato wajen biyan kudaden albashin ma’aikata da suke bi bashi.

   

  Har’ila yau ya ce jihar Filato ta amfana da tsare tsaren da gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari ta kirqiro don taimakawa al’ummar Nijeriya, musamman tsare tsaren bayar da rancen noma da shirin tallafawa daliban da suka kammala mayan makarantu na N-Power da dai sauransu.

   

  A karshen ziyarar  shugaba Buhari  ya kaddamar da taraktocin noma na jihar Filato karkashin jargorancin gwamna Simon Lalong a ranar juma’a, kafin ya tashi zuwa Abuja.

   

   

   

   

   

   

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here