Ana Ba Sanatoci Miliyan Sha Uku Da Rabi Kowane Wata – Shehu Sani

0
616
Shugaban majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

CIKAKKUN sahihan bayanai da muke samu na cewa Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya da ake kira Kwamared Shehu Sani ya bayyana irin yadda ake rabon kudin talakawa a Majalisar Dattawan Nijeriya inda ya ce ana ba su Miliyan sha uku da rabi kowane wata.

Wannan amai daga Kwamared Shehu Sani na zuwa ne lokacin da mafi yawan ‘yan Nijeriya ke cikin wani mawuyacin halin kuncin rayuwa.

Bayanai dai sun tabbatar da cewa ana biyan ‘yan Majalisar Dattawa kudi Naira Dubu dari bakwai da hamsin a matsayin albashi ban da wadannan miliyoyin da Shehu Sani ya ambata.

Abin la’akari  dai a nan shi ne ko wadanne dalilai ne za su bayar da ake yi da wadannan miliyoyin? Ga shi tun da aka kai wa ‘yan majalisar kasafin kudi har yau ba a iya yin komai a kan kasafin ba domin jama\’ar kasa sun ji shiru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here