WANI DALIBIN DA YA YI WA SARKIN KANO SOJAN GONA NA FUSKANTAR HUKUNCIN KOTU

0
718
San Kano, shugaban sarakunan arewa
Daga Usman Nasidi
WANI dalibi mai shekaru 20, Sultan Bello da ke yi wa Sarkin Kano sojan gona ya gamu da fushin wata kotun majistare da ke zamanta a jihar Kano, inda ta ba da umarnin garkame shi a gidan Kurkuku.
Alkalin Kotun Hassan Ahmad ne ya ba da wannan umarni bayan sauraron laifuka guda uku da ake tuhumar Sultan, mazaunin Ja’oji, da suka hada da sojan gona, cin amana, da kuma bata suna.
Da farin zaman na ranar Laraba 21 ga watan Maris, Dan sanda mai shigar da kara Haziel Ledapwa ya bayyana ma Kotun cewar Sultan ya aikata laifukan ne a ranar 27 ga watan Fabrairu a wani shafin Instagram da yake amfani da shi da sunan mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II.
“Ya nemi kimanin kudi Naira miliyan 1.85 daga mutanen da suka hada da; Baraka Sani ta ba shi Naira Miliyan 1.4, N150,000 daga Sadiq Saflan, N50,000 daga Sadiq Sani, N50,000 daga Aisha Ahmad, N50,000 daga Surajo Zakari da kuma N150,000 daga Yahaya.”
Dan sandan ya kara da cewa Sultan ya nemi wadannan kudade ne da nufin biyan wata mawakiyar fina-finan Hausa mai suna Zubaida Mu’azu da ta yi masa waka, a matsayinsa na Sarkin Kano, inda ya ce su tura kudaden zuwa asusun banki mai lamba 3049986447, bankin First Bank.
Daga karshe Dan sandan ya ce hakan ya saba wa sashi na 132, 322 da 392 na kundin hukunta manyan laifuka. sai dai a zaman na ranar Laraba, Sultan ya amsa dukkanin laifukan da ake tuhumarsa, bayan nan kuma Alkali ya dage sauraron karar zuwa 26 ga wata Maris.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here