KAFEWAR DAM NA GWARANYO: Rayuka Miliyan Hudu Suna Neman Tallafi

  0
  883
  Gwamna Aminu Waziri Tambuwal sha kwaranniya

  KAFEWAR DAM NA GWARANYO: Rayuka Miliyan Hudu Suna Neman Tallafi

  KIRA NE NA GAGGAWA GA GWAMNATIN TARAYYA

  Daga Zubair Abdullahi

  DAM na Gwaranyo wuri ne da ke zaman matattarar ruwa na hukumar Rafukan Rima da yake da yake a karamar hukumar Gwaranyo da take a Jihar Sakkwato a Arewacin Najeriya. An gina wannan Dam ne har kammala shi a shekarar 1984. Rafuka irin su Rafin Gagare da Rafin Bunsuru da Rafin Maradi su ne rafukan da suka ratsa cikin Dam na Gwaranyo. A yayin da ake gina Dam din sai da ya shafi kauyuka fiye da 30 wadanda aka canza masu matsugunni, kauyukan nan na da mutane sama da Dubu 18. Matattarar ruwan da Dam din ya samar shi ne na biyu mafi girma a Najeriya da dan Adam ya gina, yana da girman kilomita 200 (20,000 ha ) da ke iya tattara ruwa ‘cubic meters’ 976. Dam din ginin kasa ne mai tsawon mita 21 da jimlar fadin kilomita 12.5. Dam din abin alfahari ne don ci gaban ma’adinan ruwa ga shirin noman rani na Middle Rima da na FADAMA wanda ya somo daga kauyen Katsira zuwa Rafin Mouth a Yalwa-Yawuri zuwa wuraren Gwaranyo da Argungu da yake da girman 17000 ha. A matsayinsa na Dam babba yana taimakawa wajen ambaliyar ruwa ya kuma bayar da ruwan noma ‘cubic meters Miliyan 425, sannan shi ne ke bayar da ruwan amfani a gidajen jama’ar Jihohin Sakkwato da Kebbi a sashen Arewa maso Gabas na Kebbi, uwa-uba kuma Dam din na Gwaranyo yana amfanar da masu Su (kamun kifi ) da kuma masu yawan shakatawa.

  A takaice dai za a iya cewa tsirar da rayukan al’umma Miliyan hudu na Jihohin Sakkwato da Kebbi shi ne daidaituwar wannan Dam. A watan Agusta 2010 an yi wani mamakon ruwan sama wanda ya cika Dam din makil, da aka yi yunkurin a rage ruwan, sai ruwan ya balle ya sami kofa a RANAR 1 GA WATAN Satumba, 2010 inda ya kawo ambaliyar ruwa a kauyen Kagara. A wannan wata na Satumba 2010, bangarori da dama na Dam din suka balle aka sami karuwar ambaliyar ruwa. An gano cewa, yanayi ne mai tsananin zafi tare da samun ruwan sama mai yawan gaske, hakan ya kawo kauyuka da dama ne ambaliyar ruwan ta shafe su.

  Haka kuma a ranar 18 ga watan Maris 2018, Gwamnan Jihar Sakkwato Rt Honorabul Aminu Waziri Tambuwal ya koka kan karancin ruwan a Dam na Gwaranyo, inda ya nemi masu ruwa da tsaki da su hada karfi da karfe wuri daya domin a shawo kan matsalar karancin ruwan wanda ya ce ya ragu kwarai har kusan kasha 90 cikin 100. A wata ziyarar gani da ido da ya kai tare da manyan  jami’an gwamnati, Gwamnan ya ce, ‘’ Matattarar ruwan na Dam din Gwaranyo an gina shi ne don ya ajiye ruwa cubic meters Biliyan daya, amma kamar yadda muke gani a yau, ruwan da ke cikinsa kimanin cubic meters 100 ne kawai. Wannan ne ya kawo karancin rarraba ruwa da hukumar ruwa take yi, inda muka koma muna bayar da ruwan jifa-jifa ga mutane. Manomanmu ma suna shan wahala domin abin da noman raninsu zai samar ba zai zamanto wani abin-a-zo-a-gani ba’’.

  Manajin Darakta na hukumar SRRBDA, Injiniya Buhari Bature ya nuna cewa, kafewar Dam din shi ne mafi muni da suka gani a cikin shekaru sama da 25. Sai ya danganta matsalar da karancin ruwan sama da aka samu a shekarar 2017 da ma canjin yanayi.

  Injiniya Buhari ya ci gaba da kira yana cewa, ‘’ Muna kira  tare da rokon wadanda suke da ruwa da tsaki kan wannan al’amari, musamman ma Fadar Shugaban Kasa da su shige gaba don ganin an farfado da wannan Dam muhimmanci, musamman ma idan aka yi la’akari da yawa-yawan al’ummomin da suka dogara kacokan wajen amfani da ruwan domin biyan bukaatunsu nay au da kullum ciki har da samun kudaden shiga’’.  Gwamna@AWTambuwal

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here