Shugaba Buhari Ya Je Jihar Zamfara Domin Jajanta Wa Al\’umma

0
740
Shugaba Muhammadu Buhari

Rabo Haladu Daga Kaduna

SHUGABA  Muhammadu Buhari  ya ziyarci  jihar Zamfara
Ya je jihar ne a ci gaba da ziyarar da yake kai wa jihohin da ke fama da matsalolin rashin tsaro.
Shugaban ya jajantawa \’yan jihar ta Zamfara saboda hare-haren \’yan fashin shanu da suke
fama da su.
A makon jiya ne shugaban na Najeriya ya kai ziyara jihohin Taraba, Binuwai da Yobe wadanda ke fuskantar kabulaben tsaro.
Shugaban ya gana da sarakuna da shugabannin yankuna daban-daban da kuma masu ruwa da tsaki na jihar.
Ko da a watan jiya sai da Shugaba Buhari ya bayar da umurnin gaggauta tura sojoji zuwa jihar bayan wasu da ake zargi \’yan bindiga ne sun kashe mutane 35 a harin da suka kai a kauyen Birane cikin karamar hukumar Zurmi.
Wani dan majalisar dattawan Najeriya da ke wakiltar Zamfara Sanata Kabiru Marafa ya yi
zargin cewa gwamnan jihar Zamfara Abdul\’aziz Yari ya san \’yan bindigar da ke kai hare-hare a jihar amma ya ki daukar mataki a kansu. Sai dai gwamnatin jihar ta ce wannan zargi bashi da kanshin gaskiya.
A farkon watan nan gwamnatin jihar ta tabbatar da kashe Buharin Daji, mutumin da ake zargi da jagorantar barayin shanun da suka addabi jihar da hare-hare

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here