GIRBIN AMFANIN GONA AN KASHE MUTUM BIYAR A KUROS RIBA

0
726
I G Na \'Yan Sandan Najeriya
MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba
AKALLA mutum biyar aka kiyasta sun sheka lahira a wani rikicin
amfanin gona da  tsakanin al’ummar Beebo da makwabtansu Okwabang,
kauyuka ne da ke gabashin karamar hukumar Boki,jihar Kuros Riba kuma
suke makwabtaka da juna gidaje masu dimbin yawa aka ce an kone a
fadan da girbi ne  ya haddasa.Yadda fadan ya samo asali kamar yadda
wani mutumin Beebo ya shaida wa wakilinmu bisa sharadin kada a ambaci
suna ya ce “Ranar Talata ce shugaban matasa wani mai suna Manjok suna
yawon sintiri sai suka yi zargin sunga wani mutumin kauyenmu “Beebo
yana girbin amfanin gona na mutumin kauyen Okwabang daga nan ne sai
cacar baki ta fara abu kamar wasa har lamari ya kazance ya kai ga
sauran kone-kone da kuma asarar rayuka ni dai na ga gawar mutum biyar da
idona ni ma da kyar na tsere na kama hanya ta zuwa Kalaba wurin ‘yan uwa
kafin kura ta lafa in koma gida”.inji shi.
Fada tsakanin al’umomin biyu sun shafe shekaru masu dammar gaske suna
gwabzawa tsakani  kauyuka ne da Allah huwace musu kasar noma bayan
noman koko suna noma sauran amfanin gona dangin su gero masara da kuma
doya wakilinmu ya  tuntubi Hafiz Muhammad Inuwa kwamishinan ‘yan
sandan jihar Kuros Riba game da lamari ya ce mutum uku ne suka rasa
rayukansu amma qura ta lafa sakamakon tura jami’an tsaro da akayi
kowa kuma ya koma bakin harkokinsa  .Haka nan kuma kwamishinan ya ce
“an kama mutum uku da ake zargi da haddasa fitinar ana nan ana
bincike”.
Ya zuwa rubuta wannan labara hankula sun kwanta al\’umomin kowa ya ci
gaba da yin girbin amfanin gonarsa a wasu lokuta irin wannan a jihar
Kuros Riba idan damina ta fadi aka yi kokarin girbe amfanin gona ana
mayar da wani.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here