Gobe Za A Yi Jana\’izar Sojoji Sha Daya Da Aka Kashe

0
681
Ina Sojojin Suke Ne? Boko Haram A Yobe
Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

RUNDUNAR sojan Nijeriya ta daya da ke da mazauni a Kaduna ta bayyana cewa a gobe idan Allah ya kai mu za ta gudanar da Jana\’izar Alfarma irin ta soja domin karrama sojojin da suka rasa ransu lokacin suna gudanar da aikin kare kasa a Kaduna.
Rundunar sojan ta daya ta bayyana hakan ne a cikin wata takardar da suka raba wa manema labarai a garin Kaduna mai dauke da sa hannun jami\’in hulda da jama\’a na rundunar Kanar Muhammad Dole.
Sun dai bayyana cewa za a binne sojojin ne a makabartar sojoji da ke cikin garin Kaduna ranar 29 ga watan Maris 2018 da misalin karfe goma na safe in Allah ya so.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here