SHUGABAN LIMAMAI YA NUNA TAKAICINSA GAME DA YADDA MATASA SUKE LALACEWA

0
648
Exif_JPEG_420
 MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga kalaba
SHUGABAN kungiyar Limamai da Alarammomi ta jihar Kuros Riba Kyaftin Rirwan Liman ya nuna takaicin sa matuka gaya yada matasa a kudancin kasar nan suka lalace da shaye-shayen miyagun kwayoyi da kuma shiga kungiyoyin asiri da sauran nau\’ukan ta’addanci.
Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da ya yi jawabi wajen walimar yaye daliban makarantar Nurul Islam da ke Nasarawa-Bacoco karamar hukumar birnin Kalaba, Jihar Kuros Riba da suka sauke Alkur’ni .
Ya ce matasa “yanzu sun rungumi shan kayen maye maimakon su rungumi tafiya makaranta neman ilmin addini dana zamani amma abin takaici yaran nan sai ka ga sun jefa kan su cikin ayyukan ta’adanci musamman ‘ya’yanmu na nan Kurmi yau kungiyar asiri su ne shan kayan maye sun fi kowa zarra wannan abin takaici ne”inji shi.
Shugaban kungiyar Limaman ya ci gaba da cewa “abin bakin ciki yau maimakon a ga yara matasa sun sauke Alkur’ani ana walimar su kamar yadda ake yi a wannan makaranta yau yawan daliban da za a yaye (sauke) ya fi yawan maza abin takaici mata 17 cikin su namiji daya ne ya sauke, sauran takwarorinsa kuwa kowa ya rungumi kallon kwallo maimakon
daukar  littafi a tafi makaranta”.
Da ya juya kan iyayen yara kuwa Kyaftin Liman ya hore su da su guji nuna wa ‘ya’yansu soyayya wadda wasu iyayen kan kasa tsawatarwa ‘ya’yansu .
Hasashen da limamin ya ce an yi an gano yawancin yara matasa musulmi da ke Kurmi musamman Kuros Riba sun watsar da zuwa  makarantun Islamiyya mata ne suka fi yin hanzari da son neman ilmin addini.
Karshe ya nuna matukar takaicinsa ya matasa yadda yara matasa a kurmi suka
lalace.
Makarantar Nurul Islam ake Nasarawa-Bacoco, karamar hukumar birnin Kalaba Jihar Kuros Riba ta yaye dalibai goma sha takwas da suka sauke Alkur’ani mai tsarki a karshen makon da ya gabata. ‘Yan mata 17 suka sauka yayin da cikon na 18 din namiji ne daya tilo a cikin su.
A jawabin da ya yi wurin walimar sarkin Nasarawa-Bacoco Alhaji Sani Baba Gombe ya kalubalanci iyayen yara da su rika tura yaran su zuwa makaranta neman ilmin addini domin ta haka ne za su san yadda za su bauta wa Madaukakin Sarki.
A cewar Basaraken , abin takaici ne a ce a yaye dalibai 18 da suka sauke Alkur’ni amma  namiji daya aka samu a cikin su alhali ga matasa nan sai yawon banza sun watsar da zuwa makaranta su nemi ilmin addini.
Da ya juya kan iyayen yara su ma ya shawarce su da su rika fita hakkin malaman da suke karantar da yaransu.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here