AN GUDANAR DA RIGAKAFIN SANKARAU  A WASU SASSA NA KARAMAR HUKUMAR DAWAKIN TOFA.

0
728
Jabiru A Hassan, Daga Kano.
AN gudanar da rigakafin cutar sankarau a garuruwan Tumfafi da Kunnawa Majema sakamakon yawaitar mace-macen yara kanana da aka samu a wadannan garuruwa domin dakile yaduwar wannan cuta sanadiyyar zafin da ake fama da shi.
Wakilinmu wanda ya ziyarci garin Kunnawa Majema yayin gudanar da allurar, ya ruwaito cewa an sami nasarar yi wa yara  maza da mata masu tarin yawa rigakafin musamman ganin yadda aka sami yawaitar mutuwar kananan yara a wannan gari a \’yan kwanakin nan.
Sannan iyayen yara sun bai wa jami\’an kula da lafiya da suka gudanar da rigakafin cikakken goyon baya da hadin kai wanda hakan ya taimaka sosai wajen cimma nasarar wannan rigakafi tun da aka fara gudanar da ita a garin, kana su kansu jami\’an sashen kula da lafiya na karamar hukumar ta Dawakin Tofa da wadanda suka je garin daga ma\’aikatar lafiya ta jihar da kuma na sauran cibiyoyin kula da lafiya, sun yi kokari sosai wajen tabbatar da cewa an yi wa yaran yankin rigakafi domin kawar da cutar baki dayanta.
Da yake yi wa wakilin namu karin bayani, shugaban karamar hukumar ta Dawakin Tofa Alhaji Ado Tambai Kwa, ya ce sun yi kokarin sanar da gwamnatin Jihar Kano halin da ake ciki, inda ba tare da bata lokaci ba aka tura jami\’an lafiya zuwa yankunan Tumfafi da Kunnawa Majema bisa taimakawar ma\’aikatan sashen lafiya na karamar hukuma,  inda kuma aka gudanar da rigakafi da sauran bincike kan yadda za a kawar da wannan cuta da sauran cututtuka masu saurin yaduwa.
Sannan ya yaba wa dukkanin wadanda suka taimaka wajen ganin an yi wannan rigakafi ga kananan yara a garuruwan da cutar ta yi sanadiyyar mutuwar yaran,  kana ya yaba wa iyaye saboda hadin kai da suka bai wa jami\’an lafiyar da suka yi wannan aiki domin ganin an dakile cutar, tare da jaddada cewa karamar hukumar Dawakin Tofa za ta ci gaba da bai wa fannin kiwon lafiya muhimmanci.
Shi ma a nasa tsokacin, kakakin majalisar karamar hukumar, wanda kuma ya jagoranci kansilolin yankin zuwa wajen rigakafin Alhaji Garba Mudi Kuidawa, ya ce ko shakka babu an hada hannu wajen wannan rigakafi musamman ganin yadda karamar hukumar ta Dawakin Tofa take kokari wajen kula da lafiyar al\’umar yankin, sannan ya jinjina wa dukkanin jami\’an lafiyar da suka gudanar da wannan rigakafi a garin Kunnawa Majema tare da kara yin kira ga al\’uma da su rika bin shawarwarin likitoci a duk lokacin da wata annoba ta bulla.
Bugu da kari, jami\’in kula da lafiya a matakin farko na karamar hukumar ya nuna gamsuwar sa bisa yadda rigakafn ya gudana, tare da yin godiya ga majalisar karamar hukumar Dawakin Tofa saboda yadda ta dauki wannan aiki da muhimmanci, inda kuma ya yaba wa dukkanin wadanda suka halarci wannan gari na Kunnawa Majema domin yin rigakafin.
A nasa bangaren, kansilan mazabar Gargari Alhaji Abdullahi Yahaya Dungurawa ya yi  aamfani da wannan dama inda ya yi godiya ga shugaban  karamar hukumar Dawakin Tofa Alhaji Ado Tambai Kwai da mataimakinsa Alhaji Garba Yahaya Labour da kakakin majalisar karamar hukumar  Alhaji Garba Mudi da sauran kansilolin da suka halarci garin da kuma  shi kansa shugaban sashen kula da lafiya a matakin farko na yankin da jami\’an da suka gudanar da rigakafin cikin nasara.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here