ZA TA CI GABA DA BADA ILIMI MAI INGANCI

0
801

Jabiru A Hassan Daga Kano.

MAKARANTAR  islamiyya da haddar alkur\’ani  ta tunawa da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi da ke garin Zangon Mata, cikin yankin karamar hukumar Dawakin Tofa za ta ci gaba da ba da ilimi mai inganci tare da koyar da tarbiyya domin samar da al\’uma tagari.

Shugaban makarantar,  Sheikh Tasi\’u Ishaq shi ne ya bayyana haka a hirar da suka yi da wakilinmu a makarantar, inda kuma ya sanar da cewa ba da ilimi ingantacce tun daga tushe abune da yake da muhimmaci, don haka ne yayi tunanin samar da wannan makaranta  domin bada tasa gudummawar wajen bada ilimi na addinin musulunci  da na zamani da kuma tarbiyyantar da yara tun suna kanana.

Sheikh Tasi\’u Ishaq  ya kuma nunar da cewa an  bude wannan makaranta bisa jagorancin shugaban majalisar malamai ta Jihar Kano, Sheikh Falalu Dan almajiri da dalibai talatin maza da mata yau kimanin shekaru shida, domin  ganin yaran wannan gari na Zangon Mata da kewaye sun sami wani guri na samun ilimin addini da na zamani ba tare da tafiya wasu gurare neman ilimi ba.

Sannan ya ce ba shi da dangantaka da wannan yanki, amma ya kafa makarantar ne. sakamakon zuwa garin da ya yi bisa dalilin aikin noma amma da ya fahimci cewa babu makaranta a wajen sai ya mayar da gonar ta zama makaranta domin ba da ilimi da tarbiyya musamman ga yara kanana domin su kasance al\’uma tagari.

Haka kuma ya bayyana cewa yanzu akwai dalibai fiye da dari bakwai a makarantar, sannan an sanya mata suna \”makarantar  islamiyya da haddar alkur\’ani  ta tunawa da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi\” saboda irin gagarumar gudummawar da sarkin ya bayar wajen bunkasa addinin Musulunci da kuma tarbiyya ga yara masu tasowa na wancan zamani.

Dangane da halin da makarantar ke ciki kuwa, Sheikh Tasi\’u Ishaq ya sanar da cewa suna bukatar ganin an samar da karin gine-gine na ajujuwa da bandakuna da samar da ruwa da kuma kayan aiki musamman ganin cewa  wannan makaranta ta yi fice kwarai da gaske wajen koyar da karatun addini da na zamani da kuma tarbiyya tun kafuwar ta.

Bugu da kari, shugaban makaratar ya nuna matukar godiyarsa ga wani bawan Allah wanda yanzu haka yake gina masu karin ajujuwa a makarantar  domin ganin an fadada karatu a cikinta,  sannan ya yaba wa daukacin al\’umar wannan yanki da iyayen yara da malamai da ita kanta majalisar karamar hukumar Dawakin Tofa saboda goyon baya da hadin kai da ake bai wa wannan makaranta ba tare da nuna gajiyawa ba.

Daga karshe, Sheikh Tasi\’u Ishaq  ya gode wa Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje da mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na II  saboda taimakon da suke bayarwa domin ciyar da addinin Musulunci gaba,  sannan ya yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga sauran al\’uma masu iko da kungiyoyin rajin ci gaban ilimi da su taimaka wa wannan makaranta domin ta ci gaba da ba da ilimi a wannan yanki.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here