An sace amarya da \’yan rakiyarta a jihar Kaduna

0
611

Rabo Haladu Daga Kaduna

ANA ci gaba da alhinin sace wata amarya a kan
hanyarta ta zuwa gidan miji a yankin karamar
hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.
Ana zargin masu garkuwa da mutane don neman
kudin fansa ne suka sace amaryar, mai suna
Halima, tare da masu yi mata rakiya lokacin da
hanya ta biyo da su jihar a kan hanyarsu ta zuwa
jihar Neja daga jihar Katsina, bayan an daura
aure.
Angon ya shaida wa manema labarai  cewa, sun je daurin
aure ne a karamar hukumar Ingawa ta jihar
Katsina daga karamar hukumar Hushishi a jihar
Neja.
Ya ce an kammala  biki lafiya, to amma wurin
dawowa a ranar Asabar bayan an daura aure sai
muka kama hanyar koma wa jihar Neja da amaryar.
\”Mun isa yankin Birnin Gwari ne da marece kuma
a lokacin daya daga cikin direbobin motar da ke
dauke da amaryar ya fada hannun masu garkuwa
da mutanen\”.
Daga nan ne sai masu satar mutanen suka tisa
keyar amaryar da sauran \’yan uwanta da ke
mata rakiya, kamar yadda angon ya bayyanawa manema labarai cewa
Har yanzu amaryar na ci gaba da kasancewa
hannun masu garkuwa da mutanen, kamar yadda
rahotanni suka bayyana.
Sai dai rundunar \’yan sanda a jihar ta ce ba za ta
ce komai ba game da batun sa ce amaryar, har
sai ta samu gamsassun bayanai.
Wannan batun na zuwa ne a dai-dai lokacin da
ake cewa an yi sulhu da masu satar mutane a
yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here