GWAMNA GANDUJE YA CIRI TUTA WAJEN INGANTA KASUWANNI DA CINIKAYYA

  0
  860

  Jabiru A Hassan, Daga Kano.

  WANI matashin dan kasuwa da ke kasuwar kayan abinci ta duniya ta Dawanau Alhaji Abubakar Mu\’azu ya ce Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya ciri tuta saboda kokarin da yake yi wajen kyautata yanayin kasuwanci  da cinikayya a jihar ta hanyar inganta wasu manyan kasuwanni.

  Ya yi wannan tsokaci ne cikin wata zantawa da suka yi da wakilinmu a kasuwar ta Dawanau, inda kuma ya sanar da cewa a halin yanzu Gwamna Ganduje yana daukar matakai masu gamsarwa wajen farfado da tattalin arzikin Jihar Kano da samar da yanayi mai kyau ga ‘yan kasuwa kamar yadda ake gani a halin yanzu.

  Alhaji Abubakar Mu\’azu ya ba da misali da yadda Gwamnan ya kyautata yanayin kasuwar Kantin Kwari  da kasuwar Sabon Garin Kano da kuma sauran kasuwanni domin ganin ana ci gaba da kasuwanci cikin nasara da kuma riba, tare da fatar cewa gwamnatin Jihar Kano za ta sanya kasuwar Dawanau cikin jerin kasuwannin da za ta bunkasa saboda muhimmancinta a fagen kayan abinci.

  A karshe, ya yi amfani da wannan dama wajen yin jinjina ga daukacin ‘yan kasuwar ta Dawanau maza da mata da masu safarar kayan amfanin gona daga wasu sassa zuwa kasuwar da kuma shi kansa Kantoman riko na kasuwar da dukkanin wadada suke da hannu wajen ganin ana gudanar da al\’amura na cinikayya mai gamsarwa a kasuwar.

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here