KUNGIYAR IZALA ZA TA KAFA JAMI’A A NIJERIYA –SHEIKH JINGIR

0
1484
Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir.

  Isah Ahmed, Abuja

SHUGABAN majalisar malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’iKamatis Sunnah ta Kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bayyana cewa ya zuwa yanzu, kungiyar ta yi nisa wajen shirye-shiryen kafa jami’a a Nijeriya.

Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi, a wajen taron wa’azi na kasa tare da kaddamar da neman gudunmawar bunkasa ilmi da ilmintarwa na kungiyar, na wannan shekarar da aka gudanar a Abuja babban birnin tarayyar Nijeriya, a ranar Lahadin da ta gabata.

Ya ce tuni mun rubuta takarda a ba mu izini mu bude jami’a kuma an ba mu ka’idoji a zamanin wannan gwamnati ta shugaban kasa Muhammad Buhari. Don haka muna rokon gwamnatin ta ba mu goyan baya kan wannan kuduri namu na bude wannan  Jami’a.

Sheikh Jingir ya yi bayanin cewa ya zuwa yanzu wannan kungiya tana da makarantu daban daban na yara da manya har  guda 6144 da dalibai sama da miliyan 7, a kowanne lungu da sako na Nijeriya.

Ya ce idan muka yi la’akari da yawan wadannan makarantu da dalibai da muke da su, lokacin da za mu bude jami’armu ya zo, domin muna da daliban da za mu tura zuwa wannan jami’a da za mu bude.

‘’Ganin cewa babu abin da za mu bai wa al’umma ya taimake su kamar ilmi, ya sanya wannan kungiya ta tashi tsaye wajen bunkasa ilmi a Nijeriya da kasashen makwabta’’.

A nasa jawabin mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya yi kira ga al’ummar musulmi su hada kai su zauna lafiya, domin sai da zaman lafiya ne ake iya yin komai na rayuwa.

Sarkin musulmin wanda mai martaba Sarkin Keffi Alhaji Chido Yamusa ya wakilta,  ya yi kira ga al’ummar musulmi kan su tashi su  nemi ilmi, musamman ilmin kimiyya da kere kere. Ya ce babu shakka al’ummar musulmi sun sakaci kan harkokin ilmi a Nijeriya.

Don haka ya yaba wa wannan kungiya kan yadda ta kakkafa makarantu a birane da kauyuka.

Shi dai wannan taron da ya sami halartar manyan baki da suka hada da Ministan Abuja Alhaji Muhammad Musa Bello wanda ya wakilci  shugaban kasa Muhammad Buhari a wajen taron  da Sanata Isah Maina da ya wakilci Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal da tsohon gwamnan jihar Neja Alhaji Babangida Aliyu da manyan malaman kungiyar  da ‘yan kungiyar daga ciki da wajen Nijeriya.

Kuma a wajen taron an kaddamar da wani littafi mai suna tarihin kungiyar jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah  a madubin gaskiya da shugaban majalisar malamai na kasa na kungiyar Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya wallafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here