ZAN CI GABA DA  TALLAR BUHARI  DA GANDUJE  DUK DA KALUBALEN DA MUKE FUSKANTA-BASHIR DANDALAMA.

  0
  600
  MATASHIN DAN SIYASA BASHIR
  Jabiru A Hassan, Daga Kano.
  WANI matashin dan siyasa kuma jagoran matasa masu bayyana manufofin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamnan jihar kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje Alhaji Bashir Dandalama yace zai ci gaba da bayyana manufofin shugaban kasa da gwamnan kano ta kowace fuska domin fahimtar da al\’uma irin  kyawawan manufofin wadannan shugabanni biyu.
  Yayi wannan tsokaci ne cikin zantawar su da wakilin mu, tareda jaddada cewa matasan kasar nan suna gamsuwa  da yadda shugaba Buhari yake tafiyar da jagorancin wannan kasa tun  lokacin da aka zabe shi a shekara ta 2015,  sannan ya bada misalai masu yawa dangane da yadda shugaba Buhari ya sami kasarnan da irin kokarin da yake yi wajen samar da gyara sakamakon barnar da aka dade ana yiwa kasar.
  Alhaji Bashir Dandalama ya kuma sanar da cewa yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sami kasar nan abin babu dadi, don haka wajibi ne abi a sannu wajen samar  da gyare-gyare  ta yadda kowane dan kasa zai gamsu da canjin da aka samu  musaman ta fuskar tsaro da kyautata rayuwar al\’uma ta fannoni daban-daban na rayuwar ya da kullum.
  Sannan ya ce a matsayin sa na jagoran matasa a kananan hukumomin Tofa da Dawakin Tofa da kuma Rimin Gado zai ci gaba da hada kan matasan wannan yanki  domin  yin aiki da  murya daya wajen tabbatar da nasarar jam\’iyyar APC da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamnan jihar kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje  a zaben shekara ta 2019 mai zuwa  domin dorawa kan kokarin da suke yi  wajen bunkasa rayuwar al\’umomin su kamar yadda suke yi a halin yanzu.
  Bugu da kari, Alhaji Bashir Dandalama  ya  sanar da cewa Nijeriya kasa ce da take bukatar shugaba nagari kamar Buhari saboda yanayin da ake ciki ta fuskar tsaro da yaki fa cin hanci da kuma samar da aiyuka ga al\’uma a bunkasa noma da kuma tattalin arIKI, inda daga karshe ya yabawa shugaan karamar hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Ado Tambai Kwa bisa kokarin da yake yi wajen ciyar da yankin sa gaba tun lokacin da ya kama aiki.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here