2019: Buhari Zai Kara Tsayawa Takara

0
831
Shugaba Muhammadu Buhari ne yake jaddada niyyarsa ta sake tsayawa takara a 2019
  Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
SHUGABAN tarayyar Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana aniyarsa na sake tsayawa takara a zaben shekarar dubu biyu da sha tara mai zuwa.
Shugaba Buhari ya bayyana aniyarsa ne a wajen wani babban taron masu ruwa da tsaki na \’ya\’yan jam\’iyyar APC da aka yi a birnin tarayya Abuja.
Da yake ganawa da manema labarai Gwamnan Jihar Filato Barista Solomon Lalong ya ce wannan ikirari na shugaban kasa ba zai hana kowa tsayawa takara ba don haka kowa na da ikon tsayawa ya nemi kujerar shugaban kasa a cikin APC kuma a Nijeriya.
Sai dai abin dubawa a nan shi ne ko a bana ma za a sake yin zabe irin na sak? Lokaci ne zai nuna musamman idan an zo wajen yakin neman zabe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here