KUNGIYAR \”KANO TA AREWA INA MAFITA\”  TA NA NEMAN CANJIN  SANATA BARAU I JIBRIN A 2019.

  0
  764
  Sanata Jibiril
  Jabiru A Hassan, Daga Kano.
  KUNGIYAR  \”Kano ta arewa ina mafita\”, wadda kungiyoyin matasan  shiyyar kano ta arewa suka kafa ta fara laluben mutumn da zai mayegurin sanatan shiyyar watau sanata Barau I Jibrin domin samar da wakilci nagari ga yankin.
  A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar  mai dauke da sa hannun kwamared Aminu Bala Shanono,  a  karshen wani taro da kungiyar tayi, matasan sun nunar da cewa lokaci yayi da zasu samo wanda zai maye gurbin  sanata Barau Jibrin saboda gazawar da yayi wajen samar da ribar dimokuradiyya a kananan humkumomin dake mazabar sa, sannan babu ruwan sa da matasan yankin suk da irin gwagwarmayar da suka yi wajen ganin ya zamo sanatan kano ta arewa a zaben shekara ta 2015.
  Haka kuma matasan sun sanar da cewa shiri yayi nisa wajen fara zagayen kananan hukumomi goma sha uku dake shiyyar kano ta arewa domin gabatar da mutumin da zai mayegurbin sanata Barau Jibrin baya tattara sukkanin bayanai dasuka wajaba  na gazawar sa a wakilcin da yake yi wa yankin,  inda kuma suka  jaddada cewa zasu yi aiki da murya guda domin cimma wannan manufa tasu.
  Matasan na kano ta arewa sun yi amfani da wannan dama wajen yabawa gwamnan jihar kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da dukkanin shugabannin kananan hukumomi goma sha uku dake wannan mazaba  saboda yadda ake tafiyar da jagoranci na adalci batare da nuna kasala ba, inda daga karshe suka nuna takacin su kan yadda sanata Barau Jibrin ya gaza komai tun da aka zabe shi a matsayin sanatan kano ta arewa.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here