A BAR HADA SIYASA DA SHA\’ANIN TSARO-MUKTAR VGN.

0
968
Mukhtar shugaban VGN
JAMI\’IN tattara bayanai  na kungiyar banga ta kasa Muktar Abdullahi Ungogo ya shawarci gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohin kasar nan da su daina hada harkar tsaro da siyasa.
Yayi wannan tsokaci ne a wata hira da suka yi wakilin mu a kano, inda ya bayyana cewa idan har ana so a cimma kyawawan nasarori ta fuskar tsaro, sai an daina sanya siyasa a harkar tsaro musamman ganin cewa tsaro yana da matakai daban-daban kuma a kowane lokaci.
Muktar Abdullahi Ungogo ya kuma sanar da cewa yanzu zamani ya canza, sannan mafiya yawancin kasashen duniya suna kan tsarin dimokurariyya wanda dole ne sai an kaucewa hada sha\’anin tsaro da siyasa idan har ana so a sami inganta tsaro a kasashen mu.
Jami\’in binciken ya kuma bayyana cewa kungiyar su ta VGN tana aiki ne bisa sa kai, sannan an kafata ne da kyakykyawar aniyar taimakawa hukumomin tsaro wajen hanawa da kawar da  laifuka a unguwanni da sauran guraren taron al\’uma kamar yadda take yi a halin yanzu.
Daga karshe, Muktar Abdullahi Ungogo yayi amfani da wannan damar wajen isar da godiyar kungiyar ta VGN ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da majalisun kasa da kuma dukkanin hukumomin  tsaro na kasar nan bisa yadda aka hada hannu wajen inganta tsaro a kowane sako da lungu na kasar nan, tareda jinjinawa babban kwamandan  kungiyar  VGN na kasa kuma jakadan zaman lafiya Alhaji Dokta Ali Sokoto bisa kyakykyawan jagoranci da yake yiwa kungiyar batare da nuna gajiyawa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here