GWAMNA TAMBUWAL YA NADA SABABBIN JOJI-JOJI SU 4

0
1211
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal Na Jihar Sakkwato dan takarar shugaban kasa a jam\'iyyar PDP

Rahoton Zubair Abdullahi Sada

GWAMNA Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato ya rantsar da sababbin Joji-Joji su hudu wadanda za su yi aiki a Babbar Kotun jiha da Babbar Kotun Daukaka kara ta shari’a.

Gwamnan ya yi wannan nadi ne a yau Laraba a inda ya ce, dukkan wadanda aka nada sun dace da mukaman domin kwararru ne a fannoninsu da suka amsa sunansu na masu shari’a tun daga hukumar shari’a ta kasa.

Ya ce, jami’an ma’aikatar shari’a ta jihar, suna gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Ya kara da cewa, tun da ya hau karagar mulkin jihar nan bai taba cin karo ko samun wata kara ta daya daga cikin jami’an shari’a ba daga hukumar shari’a ta kasa ( NJC ) ko ma ta jiha, wato ( JSC ).

Gwamna Tambuwal ya ce , ‘’ Kimanin shekaru goma kenan ba a yi nadin sabon alkali a jihar Sakkwato ba. To, mu  wannan buki na yau a wurinmu wani gagarumin ci gaba ne aka samu domin a habbaka ayyuka da kara kwarin gwiwa ga bangaren na shari’a’’.

‘’Ina son in tabbatar maku da kuma bangaren ‘yan majalisun jiha cewa, babu wata matsala ko kadan tsakaninmu, don haka za ku samu cikakken hadin kanmu tare da goyon bayanmu kodayaushe’’.

Ya kuma ce, ‘’ Wannan wajibi ne muddin muna sa ran mu tabbatar da ci gaban dimokuradiyya a wannan kasa’’.

A yayin da yake taya su murna, Gwamna Aminu Waziri ya nuna gamsuwarsa na cewa, za su yi ayyukansu da aka aza a kawunansu bisa tsarin shari’a da martabawa da aiki tukuru kamar yadda aka sansu.

Sababbin Manyan alkalan da aka nada, su ne Kabir Ahmad da Isah Bargaja a matsayin Joji-Jojin Babbar Kotun Jiha, sai Kasimu Yusuf da Umar Liman Sifawa a matsayin Alkalan alkalan Kotun Daukaka kara ta shari’a.

Bukin rantsar da Alkalan ya sami halartar Kakakin majalisar dokokin Jihar Sakkwato, Alhaji Salihu Maidaji da Babban Cif Jojin jiha, Mai shari’a Bello Abass da Alkalin alkalan jiha, Khadi Abdulkadir Sa’idu da sauran manya-manyan jami’an gwamnati.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here